An yanke ma Shugaban NURTW shekaru 6 a Gidan yari

An yanke ma Shugaban NURTW shekaru 6 a Gidan yari

–Kotu ta yanke hukuncin duk da cewa baya nan a Kotun,abokin laifin sa sun tabbatar da cewa shugaban su ne.

– Yaran aikin sa kuma sun shaida cewa da motarshi akayi amfani kuma suna haduwa a gidan bakin shi.

–Wani mai shaida yace a lokacin harbe-harben harsasai ne harshashi ta samu wani kuma nan ya mutu take.

An yanke ma Shugaban NURTW shekaru 6 a Gidan yari

An yanke hukuncin kwashe shekara 6 a gidan yari a kan Alhaji Mukaila Lamidi, tsohon shugaban kungiyar gamayyar direbobin Najeriya,watau NURTW shiyar Jihar Oyo. Wata babban Kotu a garin Ibadan ce ta yanke masa kurkukun shekaru 6 .

Lamidi,wanda akafi sani da Auxiliary, zai kwashe shekaru 6 a gidan maza ne saboda rawan da ta taka a hayaniyar kungiyar gamayyar wanda ya janyo sakamakon rasa rayukan wasu mazauna garin Ibadan , babban birnin Jihar a ranan 4 ga watan Yuni,shekarar 2011. Sauran abokan shiga kurkukun sa sune Saheed Kareem, Abu Kareem, Kazeem Kayode da Taiwo Tijjani.

Jaridar the nation ta bada rahoton cewa mutane 5 din sun kasance su na gurfana a kotu tunda aka kamasu a shekarar 2014. Alkali mai Sharia , Jastis Eni Esan, wanda ya yanke hukuncin yace ana tuhumar abubuwan zargin da laifuffuka 3, na kisa,na aniyar kisa.

KU KARANTA : An take mini hakki,a biyani diyyan N15 biliyan – Dasuki

Game da cewar rahoton, Lauya Akeem Agbaje ya fada ma kotu cewa yana kusa da Adekunle Adedipupo, dan shekaran karshe a jami'a wanda aka kashe,a ranar da masu laifin suka shigo gareji cikin mota fijo 604 ta auxiliary da wasu motoci biyu suna harbin kan mai uwa da wabi. Shaidan yace bayan harbin ne harsasai suka ratsa marigayin,kuma nan ya mutu take. Alkalin ya ce sun ambaci auxiliary a matsayin shugaban su a wata jawabin da suka baiwa yan sanda da kuma cewan suna haduwa a gudan bakin Diamond hotel da ke Alakia Isebo,garin Ibadan.

Lauyan Auxiliary, Olalekan Ojo, yace abokan cinikinsa zasu daukaka karan.

An dade ana rigima tsakanin bangarora 2 na kungiyar gamayyar a wurare da dama a fadin kasa. A ranan laraba,11 ga watan mayu ,wasu mambobin kungiyar sun hana motoci wucewa saboda zanga zangar da sukeyi a legas saboda wani shugaban su.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel