Ta ritsa da su Kanu da Okocha a Kasar Turkiyya

Ta ritsa da su Kanu da Okocha a Kasar Turkiyya

 

– Tsofaffin yan wasan Najeriya Kanu da Okocha suna Kasar Turkiyya lokacin da aka yi yunkurin juyin mulki.

– Yan wasan sun je Kasar ne buga wani wasan Samuel Eto’o na Kamaru ya hada.

– An dage wasan dalilin rikicin da aka shiga a Kasar Turkiyyan.

Ta ritsa da su Kanu da Okocha a Kasar Turkiyya

Bayanai sun nuna cewa mutane fiye da 200 suka mutu sanadiyar yunkurin juyin mulkin da aka yi a Kasar Turkiyya a ranar Jumu’a 15 ga watan Yulin nan. Haka kuma fiye da mutane 7,500 suka samu raunuka. Rahotanni sun bayyana cewa tsofaffin yan wasan Najeriya, Kanu Nwankwo da Austin Jay-Jay Okocha suna garin lokacin da abin ya faru. Tsofaffin ‘Yan wasan na Najeriya dai sun je buga wani wasa ne da tsohon dan kwallon Kasar Kamaru ta Afrika Samuel Eto’o ya hada, an dai so a buga wasan ne a ranar 16 ga watan Yuli (Asabar kenan)a garin Antalaya na Kasar.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, yanzu ya zama dole aka daga wasan saboda tashin-tashinar da aka samu a Kasar Turkiyyan. Eto’o yayi niyyar hada wasan ne domin murnar cika shekaru 10 da kaddamar da wata gidauniyar sa mai suna Fundación Privadao. Sai dai rikicin da ya barke na Turkiyya, bai bari an ci ma wannan manufa ba. Wasu sojin garin ne dai suka yi kokarin hambarar da gwamnatin damukaradiyya mai-ci a Kasar. Kawo yanzu dai, an kama mutane kusan 1563 da suke da hannu cikin lamarin.

A SAUKE MANHAJAR MU NA Legit.ng DOMIN SAMUN LABARIN WASANNI

Sojojin dai sun yi kokarin kwace gwamnatin, inda suka rufe hanyoyin jirgi da gadajen garin. Sojojin da suka shirya wannan abu sun kira gwamnati ta saki shugaban adawar Kasar wanda yake a daure tun Yunin bara. Tuni dai aka kifar da wannan yunkuri, Firayiminista yayi jawabi cewa gwamnatin sa na kan iko.

KU KARANTA: KO KA JI ME AHMED MUSA NA NAJERIYA YACE?

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel