An gano motocin yan sanda da suka bata a garejin Makanike

An gano motocin yan sanda da suka bata a garejin Makanike

LABARAN CIKIN GIDA

AN GANO MOTOCIN YAN SANDA DA SUKA BATA

A bayan nan ne, Sufeta-Janar na yan sandan Najeriya, Ibrahim K. Idris yayi ikirarin cewa tsohon shugaban yan sandan Kasar, Solomon Arase yayi awon gaba da motocin hukumar dai-daya har guda 24. A ranar 18 ga wannan watan yayi wannan jawabi. Ya zargi Arase da dauke motocin yan sandan Kasar da suka hada da wasu BMW da kuma motar aikin sufetan Kasar; wacce ta ke ba ta jin harsashi. To sai dai, an gano motocin a wani garejin kanikawa, inda aka kai motocin domin yi masu kwaskwarima domin sabon sufetan da zai zo ya samu na hawa. Yanzu haka an bayyana samuwar motocin na BMW da ta Sufeta-Janar na Yan sandan a wani shagon gyaran motoci ana masu gyare-gyare.

KU KARANTA: ZA A KADDAMAR DA JIRGIN KASAN NAJERIYA

An gano motocin yan sanda da suka bata a garejin Makanike

 

 

 

 

 

Jaridar Vanguard ta bayyana cewa an kai motocin gyara ne a wani gareji da ake kira Auto Computers da ke Unguwar Jabi ta Abuja. Tuni ma har an gama yi ma dayar motar ta BMW fenti, dayar kuma an kai ta ne domin duba injin ta; wanda ya dade yana bada matsala tun shekaru da dama da suka wuce. Majiyar ta nuna cewa an maida motocin ne zuwa hedikwatar hukumar Yan sandan kasara a ranar Lahadin nan (17 ga watan Yuli) bayan an kammala gyaran da aka yi. Yanzu ma dai ana jiran Mukaddasshin Sufetan Kasar ne ya bada kudin aiki. Dangane da dayar motar (wacce harsashi bay a huda ta), sai an kara daukar lokaci wajen gyara tan, domin kuwa motar da na da wahalar sha’ani saboda fasahar da ke cikin ta, kuma ma dai wasu kayan jikin na ta, sai an sayo daga Kasar waje.

Solomon Arase dai ya soki Sufetan da ke kan gado dalilin yada maganar da yayi a duniya ba tare da ya binciki ainihin maganar ba. Bangaren kula da ayyuka na Hukumar yan sandan ne dai suka bada gyaran motocin, wanda da an bincika yadda ya kamata da ba a samu wannan rudani ba.

KU KARANTA: ZA A KADDAMAR DA JIRGIN KASAN NAJERIYA

Asali: Legit.ng

Online view pixel