Najeriya za ta je Gasar cin Kofin duniya - Oboabona

Najeriya za ta je Gasar cin Kofin duniya - Oboabona

– Kasar Najeriya za ta dage ta je Gasar ‘World Cup’ da za a buga Shekarar 2018.

– Super Eagles na da duk yan wasan da ake bukata domin zuwa Gasar World Cup a Kasar Russia.

Dan wasan Najeriya, Godfrey Oboabona yace yana mai kyautata zaton cewa Najeriya za ta samu zuwa gasar cin kofin kwallon duniya shekarar 2018 a Kasar Russia. Da dan wasan yake wata yar hira da Legit.ng, ya bayyana cewa Kasar za ta samu zuwa Russia domin gasar World Cup na 2018. Yace yana sa ran Kasar ta ci wasannin ta na zagayen farko. Da yardar Ubangiji, Najeriya za ta samu zuwa Gasar cin kofin duniya… Inji Oboabona.

 

Najeriya za ta je Gasar cin Kofin duniya - Oboabona

 

 

 

 

 

 

 

Da yardar Ubangiji, Najeriya za ta samu zuwa Gasar cin kofin duniya… Za mu fito, za mu kai Russia, Mutanen Najeriya za su yi alfahari da mu. Tabbas! Za mu saka masu farin ciki. Muna da duk abin da ake bukata wajen samun nasara. Kai, Najeriya fa za ta je Gasar World Cup. Inji Dan wasan bayan Najeriya Geofrey Oboabona.

Kasar dai na cikin wani tsaka-mai-wuya, inda suke duro na B na isa zuwa Gasar. Kasar ta Najeriya za ta fafata tsakanin ta da makwabta Kamaru, ‘Chipololo’ na Kasar Zambiya, da kuma Algeriya ta Larabawa. Wanda ya samu yin nasara ne zai je Gasar ta World Cup da za a buga a Kasar Russia, nan da Shekaru 2 masu zuwa. Yanzu haka dai Kasar ta kara lulowa kasa a jerin Kasashen duniya a Kwallon kafa, inda ta rasa mataki 9 daga wancan watan, yanzu dai Najeriya ce kasa ta 70 a duniya wajen kwallon kafa.

Ko da yake dai Kasar ta Najeriya ba ta buga wani wasa ba a wannan watan, sai dai an buga Gasar EURO ta Nahiyar Turai da kuma COPA AMERICA ta Nahiyar Amerika. Kasashen da suka yi nasara a wannan gasa dai sune Portugal da Chile.

KU KARANTA: NI ZAN TARBI SHUGABAN FIFA BA PINNICK BA-GIWA

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel