Gwamnoni biyar da Buhari ke ganin girmansu (hotuna)

Gwamnoni biyar da Buhari ke ganin girmansu (hotuna)

-Shugaban Muhammadu Buhari na da zabinsa kamar ko wani dan Adam

-Gwamnoni biyar cikin gwamnonin jihohi 36 sun fi soyuwa ga Mutun na farko a kasar Najeriya

-Yana iya zama ra’ayi ne yasa shugaban kasa ya nuna sha’awa kan wadanan gwamnoni mafi soyuwa ga Buhari

Ba laifi bane don ka fi son wani mutun da wani. Akwai wasu haske da ke sa mutun yaso yin aiki da wani mutun, kuma yaji baison yin aiki da wani. Duk da haka, wasu dalilai na da wuyar faduwa kan dalilin da yasa mutun ke son wani mutun kuma sai yaji baijin dadin kasancewa da wani mutun.

1.Ibinkunle Amosun (gwaman jihar Ogun) mutanen jihar Ogun sun fi kiran gwamna Amosun da ‘SIA’. SIA na matsayin Sanata Ibinkunle Amosun.

Tsohon dan majalisar ya kasance masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari lokacin da suke jam’iyyar All Nigerian Peoples Party (ANPP) a shekara ta 2000. Dukkan su biyu sun nemi kujerar gwamna da shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ANPP amma basu kai labara ba.

Daya daga cikin hanyar da shugaban kasa ya nuna soyayyar sag a gwamnan jihar Ogun shine ya kai wa Amosun ziyara a jihar Ogun a yan wattani da suka wuce.

Gwamnoni biyar da Buhari ke ganin girmansu (hotuna)
Gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun

2.Aminu Bello Masari (gwamnan jihar Katsina) gwamna Masari ya kasance tsojon kakakin majalisar wakilai. Gwamnan jihar Katsina ya tsawa shugaban kasa lokacin da ya fito takarar shekara ta 2011.

A matsayin shugaban kasa wanda ya fito daga Jihar Katsina, Buhari bazai taba wasa da wanda ke shugabancin jihar ba, mussaman yayinda mutumin yake da tunanin irin nashi a harkan siyasa, kuma suka kasance a jam’iyya daya.

Gwamnoni biyar da Buhari ke ganin girmansu (hotuna)
Gwamnan jihar Kastina  Aminu Masari

3.Kashim Shettima (gwamnan jihar Borno) ya kamata a kira shi ‘gwamna mai rayuwa tara.’ Dalili shine gwamnan ya kokarta gurin yaki da mayakan Boko Haram na tsawon shekaru biyar.

Shugaban kasa Buhari ya ziyarci jihar Borno lokuta da dama kuma ya ba gwamnan tabbacin cewa yana tare da shi a koda yaushe domin gannin sun dawo da jihar cikin jindadi kamar yanda take kafun yan ta’addan sun dakushe jihar.

Gwamnoni biyar da Buhari ke ganin girmansu (hotuna)
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima

4.Abdulaziz Yari (gwamnan jihar Zamfara) gwamna Yari shine shugaban gwamnonin Najeriya.

Za’a iya cewa Yari na daya daga cikin yan hannun daman Buhari cikin dukkan gwamnonin Arewa. Shugaban kasa Buhari ya yarda da gwamnan jihar Zamfara da har ya zabi jihar sa a cikin daya daga cikin tsirarun gurin da ya kai ziyara a water Yuli.

Gwamnoni biyar da Buhari ke ganin girmansu (hotuna)
Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari

5.Abiola Ajomobi (gwamnan jihar Oyo) gwamna Ajimobi na iya kasance wa a cikin bakin takardar ma’aikatan jihar Oyo kan rashin nuna kula kan jin dadinsu.

A dayan bangaren, yana cikin littafi mai kyau na shugaba Buhari. Wannan ya askance saboda yaci abinci, ya fadi ya tashi tare da Buhari lokacin da suke jam’iyyar ANPP, wanan yasa shugaban kasa ya kasa mantawa da shi.

Gwamnoni biyar da Buhari ke ganin girmansu (hotuna)
Gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel