Aikin Arsene Wenger nake so- Thierry Henry

Aikin Arsene Wenger nake so- Thierry Henry

Shararren tsohon dan wasan Arsenal Theirry Henry ya jaddada burinsa na ganin ya horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal duk da cewa kungiyar taki amicewa ta bashi aikin.

 

Aikin Arsene Wenger nake so- Thierry Henry
Henry lokacin da yake aiki a Arsenal

Dan asalin kasar Faransan yayi aiki tare da kananan yan kwallon Arsenal a kakar wasa da ta wuce a sa’ilin da yake kokarin samu takardun horaswa daga FIFA. Daga bisani kuma Arsene Wenger ya bashi mukamin aiki tare da masu horar da yan kasa da 18.

Sai dai kuma maigidan Henry Arsene Wenger ya matsa kan cewa sai dai Henry ya saki aikin da yake yi na tsokacin wasanni a Sky Sports kafin ya bashi aiki kwakkwara a kungiyar Arsenal, wanda kuma Henry ba shi da niyyar yin hakan.

Duk da cewa ya saki dan aikin da yake yi a kungiyar, Henry na da yakinin zai horar da tsohuwar kungiyar tasa a nan gaba, kuma yana so ya kammala samun lasisin horaswa na FIFI mai mataki na 2.

“karya ne idan nace maka bani sha’awar zama koci, saboda ina son Arsenal matuka,” haka Henry ya fada ma jaridar Sun. “ina matukar kaunar wasan kwallo, kuma zan ci gaba da son kwallo. Ina son horar wa-sai dai lokaci bai yi ba. “duk da cewa zan iya horar da kowani kungiya, ina son in kammala samun lasisin horaswa na UEFA Pro wanda yanzu haka nake kanyi, kuma zai kara min ilimi sosai na bai daya.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel