Buhari ya jaddada goyon bayansa ga Erdogan

Buhari ya jaddada goyon bayansa ga Erdogan

-Shugaba Buhari tofa albarkacin bakinsa dangane da yunkurin juyin mulkin Turkiyya

-Shagaban ya jaddada goyon bayansa ga shugaba Erdogan

-Ya kuma taya shi murnar murkushe yunkurin juyun mulkin

 

Shugaban Najeriya ya shiga jerin shugabannin kasashen duniya wajen yin Allah wadai da yunkurin juyin mulkin da aka yi a Turkiyya wanda ya hallaka mutane 265.

A wata sanarawa da fadar shugaban ta fitar a ranar 17 ga watan Yuli, wacce kuma babban mai taimakawa shugaban a kan kafofin yada labarai, Malam Garba Shehu ya sa hannu ta ce, shugaba Buhari ya bayyana matsayinsa akan al’amuran da ke faruwa a Ankara babban birnin Turkiyya da Santanbul da kuma sauran garuruwan kasar, ya na mai nuna matukar bakin cikinsa da rahotannin yunkurin kwace mulki daga gwamnatin Tayyib Erdogan wacce aka zaba, da karfin tuwo a kasar.

KU KARANTA:Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Kasar Turkiyya

Buhari ya jaddada goyon bayansa ga Erdogan
Shugaba  Mohammadu Buhari, tare da Recep Tayyip Erdogan a fadar Villa a Abuja,

Shugaban a cewar sanarwar na cewa, “Ba za mu yarda da duk wani yunkuri na tumbuke wata gwamnati ta aka kafa ta hanyar dimukuradiya ba da karfin tsiya. Domin amfani da karfi ba ya maganin matsala illa ya dagulata, tare da mayar da hannun agogon mulkin dimukuradiyya baya”.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, shugaba Erdogan na daya daga cikin aminan Najeriya kuma masu mara mata baya a yakin da ta ke yi da ta’addanci, sannan shugaban ya yi kira da a yi tir, tare da kin abubuwan da za su rusa mulkin dimukuradiyyar kasashe ta hanyar juyin mulki a wannan karni na 21             

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel