Shege ka fasa: Dino ya shiga unguwar su Tinubu a Legas

Shege ka fasa: Dino ya shiga unguwar su Tinubu a Legas

A wata yunkuri da ke nuna tonan fadan Bola Tinubu,Sanata Dino melaye yaje Jihar Legas ya karashe makon.

Yanke shawaran melaye na ziyartar Jihar Legas a wata lokacin da yak e fukantar matsaloli da ‘yan jam’iyyar sa ta APC. Kwanan nan sanatan ya shiga rashin jiyuwa da matan tsohon gwamnan Jihar Legas, Sanata Oluremi Tinubu, yasa mutane sunce dino bai isa ya shiga Jihar Legas ba.

Shege ka fasa: Dino ya shiga unguwar su Tinubu a Legas

An bada rahoton cewa Dino Melaye yayi Magana batanci ga Sanata Tinubu a wasa musu da suka a majalisar dattawa inda yayi barazanar zai doke ta kuma yayi mata ciki kuma ba abinda zai faru. Wannan barazanar ta tayar da zaune tsaye a APC,musamman a Jihar Legas da suka gargadi Melaye da yayi hattara da zagin matan babban jigon APC.

Sanatocin jihar legas, Bareehu Olugbenga Ashafa (APC,mazabar Legas ta gabas) and Solomon Olamilekan Adeola (APC,mazabar Legas ta yamma), sun gargadi dino melaye da yayi hattara ,ya kiyayi kansa. Wannan maganar ta sa ana shakkar ziyarar shi Jihar Legas.

Amma abin mamaki,a ranar asabar ,16 ga watan yuli, sai ga Dino Melaye a Jihar Legas. An samu hakan ne ta hotunan da ya watsa shafin sada zumuntarsa  ta Twita.

KU KARANTA : Jam’iyyar APC ta kara yi ma Dino Melaye kaca-kaca

Abinda yafi ban mamaki ma, melaye unguwar Tinubu ya je,Bourdillon, kuma yace gashi nan a Jihar Legas,shege ka fasa. Idan dai zuwarsa unguwar da tinubu ke zaune,inda aka ma bola tinubu da lakabin ‘Zakin bourdillon’ tau lallai Dino Melaye yayi fito na fito da jigon APC.

Yace:

Sanarwa“Gani nan a Jihar Legas,wadanda suka ce kada in shigo , zanyi yawo a mota mara rufi a jihar”. Ga dino a titin Bourdillon a Jihar Legas yanzu,ina jiran masu surutai. Ina kuke?

Asali: Legit.ng

Online view pixel