Renieri ya bayyana makomar Riyad Mahrez

Renieri ya bayyana makomar Riyad Mahrez

Mai horar da kungiyar kafa ta Leicester City Claudio Ranieri ya fito fili ya bayyana makomar shahararren dan wasan nan nasa Riyad Mahrez.

Renieri ya bayyana makomar Riyad Mahrez
Okazaki, Mahrez and Vardy of Leicester City

Shi dai Mahrez din ana rade-raden cewa zai koma kungiyoyi da dama duk kuwa da yadda kungiyar da sa ke kokarin ganin ta inganta kwantaraginsa da zummar ganin bai tashin ba. A kakar wasannin da ta gabata dai Mahrez ya zura kwallaye 17 yayin kuma da ya taimaka wajen zura wasu 11 wanda hakan ne ya taimaka ma kungiyar tasa ta Leicester wajen lashe kofin firimiya din.

Dan kasar ta Algeria dai ya sabunta kwantaragin sa da Leicester city a watan Agustan bara inda yanzu haka yake karbar £35,000 a duk sati. Manyan kungiyoyi irin su Barcelona, Arsenal da ma PSG duk sun suna sha'awar su ga dan wasan.

Mai horarwar na Leicester City Ranieri dai kam ya bayyana cewa dan shekara 25 din zai zauna a kungiyar sa. An ruwato yana cewa: "Ni ina da yakinin cewa zai tsaya, yana son ya tsaya ma. Yana jin dadin wasa a nan kungiyar. Ko kusa ba irin yan kwallon nan bane da zasu ce suna so su tashi. Nasan ba zai bar ni ba. Yana jin dadin nan kungiyar"

Asali: Legit.ng

Online view pixel