Rayuwa a Man Utd Karkashin Jose Mourinho-Michael Carrick

Rayuwa a Man Utd Karkashin Jose Mourinho-Michael Carrick

Dan wasan tsakiya na Kungiyar Man Utd, Michael Carrick yayi magana game da sabuwar rayuwa a Kungiyar Man United da sabon koci Jose Mourinho.

– A wannan Larabar ne sabon Kocin na Man utd ya fara aiki a filin wasa.

– Jose Mourinho zai buga wasan sa na farko a gida a ranar 3 ga watan Agusta.

– Dan wasa Carrick yana da ta cewa game da Sabon Koci Jose Mourinho

Dan wasan tsakiyar kungiyar Man Utd, Michael Carrick yayi magana dangane da abin da ya shafi makon farko karkashin sabon mai horaswa, Jose Mourinho. Koci Jose Mourinho ya jagoranci horaswar farko a kulob din wannan Larabar, tare da wasu manyan yan wasan Kungiyar. Mourinho zai buga wasan gida na farko tsakanin sa da Kungiyar Everton a ranar 3 ga watan watan Agustan gobe. Za dai a buga wasan ne domin dan wasa Wayne Rooney.

Michael Carrick, na daga cikin manyan yan wasan na Man Utd. Yayi magana game da satin farko tare da sabon koci Jose Mourinho. Dan wasa Carrick ya bayyana makon farko karkashin Jose Mourinho da zad dadi. Carrick yace: “Aiki da shi ba dai dadi ba! Mun zo ranar Laraba, yanzu makon mu daya muna aiki da sabon Kocin kenan, abun ba dai dadi ba. Abun kuma babu wuya kamar yadda mutane ke tunani”. Carrick ya kara da cewa: “Ana kwallo, kuma ana raha wasu lokutan. Ina tunani kowa na murna. Idan aka ce maka an samu sabon koci, sai komai ya canza; saboda ka ga an kawo sabon mutum, mai kuma sababbin akidu. Haka nan za mu shirya fafatawa…”

Dan wasan na tsakiya yace amfanin aikin da suka yi a makon farkon shine shirya ma gasar da ke zuwa, dole kowa ya kintsa ya dawo daidai, domin tunkarar gasar da ke zuwa gadan-gadan.

KU KARANTA: JOHN TERRY ZAI YI ZAMAN SA A MATSAYIN KYAFTIN

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel