Yan daba sun sari dan Jarida a Legas

Yan daba sun sari dan Jarida a Legas

Legit.ng ta bada rahoton cewa yan tayar da kayar baya sun afka wa yan zanga zanga sun sari dan jarida. Sodiq Adelakun a Jihar Legas. Manema labaran mu da ke wurin sun shaida cewa an cikin zanga-zanga akan Koran ma’aikatan banki da aka yi ,da kuma dokar hana saye da sayarwa akan titinan Jihar Legas

Mutane da dama,da kungiyar kwadago ta Najeriya watau NLC na gudanar da zanga-zanga a gaban ginin kungiyar Nigeria Employers Consultative Association (NECA) da ke Alausa,a Jihar Legas. Kawai sai ga yan sara suka kimanin 50 sun afo wurin da makamai kala kala.

Yan daba sun sari dan Jarida a Legas

Masu zanga-zangan suka fara neman mafaka, amma wasu sun sha mumunan duka ,kuma daya daga cikinsu shine dan gidan Jaridar Punch. A lokacin da muke tattaren wannan labaru dai bamu san lafiyan shi ba,amma mutane sun ce da wuri aka kais hi asibiti.

Legit.ng ta sake bada rahoton cewa wasu yan jaridan da ke wurin ma sun sha nasu rabon bugun,kuma aka kwace kayan aikinsu. Wani wanda ke wurin yace: “yan jarida daga gidajen talabijin ya shafe su. Ko sun tsira ba tare da lalacewan kayan aikinsu ba,ban sani ba.

KU KARANTA : Jihar Legas za ta samar da wuta ta hanyar dattin bola

Game da cewar rahotanni, dan jaridan ya fara samun lafiya ,bayan wasu abokan aikinshi sun kaisa wani asibiti bayan hayaniyar

Asali: Legit.ng

Online view pixel