Avengers: Matan Gbaramatu zasu yi zanga-zanga a Abuja

Avengers: Matan Gbaramatu zasu yi zanga-zanga a Abuja

Mata daga masarautar Gbaramatu ta jihar Delta wadda ake takaddama sun fadi ra'ayinsu game da kama 'ya'yansu da hukumar hadin kan tsaro ta wucin gadi keyi yayin da suke farautar 'yan Neja Delta Avengers a cikin masarautar

Avengers: Matan Gbaramatu zasu yi zanga-zanga a Abuja
The protesters took over streets in Enugu

Matan wadanda suka karade garin Warri ranar Laraba sun ba gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro wa'adin kwana bakwai su saki 'ya'yansu, suna masu cewa wadanda aka kama ba 'yan avengers bane, yaran Gbaramatu ne marasa laifi.

KU KARANTA : Tsagerun Neja Delta sun sake fasa bututun mai

Shugabar matan Ijaw ta kasa Mrs. Veronica Tambowei, ta ba gwamnatin tarayya wa'adin kwana bakwai su saki 'ya'yansu ko ta fuskanci wata zanga-zangar a Abuja domin ganawa da shugaba Buhari, tana mai cewa idan aka kashe yaran, to hukumomin soja suyi shirin kashe su da'ya'yansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel