Nani ya kammala shirye-shiryen komawa Valencia

Nani ya kammala shirye-shiryen komawa Valencia

-Dan kwalllon na Portugal zai koma ne ka fam miliyan 7

-Nani na daya daga cikin wadanda suka ciwo gasar zakaru ta  Euro 2016

-Dan wasan ya yi farin jinin rawar ta musamman da zaran ya ci kwallo

 

Nani ya kammala shirye-shiryen komawa Valencia
Nani na cashewa da rawar gargajiya ta Barazil

Dan wasa Nani na kulop din Portugal International ya kammala shirye-shiryen komawa Valencia ta kasar Spain.

KU KARANTA: Ga fa wanda zai zama sabon mai horarwar kasar Ingila

Ana sa rai tsohon dan wasan gaba na Manchester United wanda ke burge ‘yan kallo da salon rawar gargajiya Capoeira ta Barazil, ya na mai fatan cin balalbalai da kuma yin adungure na murnar zura kwallo a sabon kulop din.

KU KARANTA: An fitar da sunayen ‘yan wasan Najeriya a Olympics

A hirarsa da shafin turancin na Valencia a internet, Nani ya na mai cewa; “Wannan wata rana ta musamman ce a gare ni da zan bugawa wannan babban kulop kwallo wanda na ke fatan kasancewa da su na shekaru masu yawa.”

Dan wasan ya yi godiya ga Suso da kuma Kim koh shugabanin kulop din da suka nuna sha’awarsu a kan sa, da har suka dauke shi, sannan ya sha alwashin yin aiki tukuru da kuma jefa kwallaye masu yawa a raga.

Nani ya kammala shirye-shiryen komawa Valencia

Nani na daya daga cikin zakarun ‘yan kuolp din Portugal da suka ciwo gasar zakarun Euro 2016 a Faransa, mai alfarin takalmin azurfa da Ronaldo ya mika mi shi, Nani ya ce yana matukar son rawan garagijya ta Barazil a duk lokacin da ya zura kwallo a raga.

 

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel