Darajar Naira ta dan farfado a kasuwar bayan fage

Darajar Naira ta dan farfado a kasuwar bayan fage

Rahotannin da ke zuwa mana a yau Alhamis 14 ga watan Juli suna nuna cewa darajar Naira ta dan farfado a kasuwannin bayan fage da naira 1 kacal. Kawo yanzu dai yan Najeriya da yawa na kokawa game da sabon tsarin da babban bankin kasar nan watau CBN ya fitar wajen cinikayyar kudaden tare da chanjin su.

Darajar Naira ta dan farfado a kasuwar bayan fage

A ta bakin wasu masu sana'ar canjin kudin da suka zanta da jaridar Legit.ng sun bayyana mana cewa a yau an tashi ne ana canjin $1 a kan N355 sabanin jiya da aka rika canjin nata akan kudi N356. Jami'an suka kara da cewa duk da ma akwai cece-kucen da akeyi game da wani rudani dake shirin kunno kai a kasuwar canji, amma suna da yakinin cewa hakan ba zai yi wani muhimmin tasiri ba a kan darajar Naira din.

Haka zalika daya daga cikin masu sana'ar canjin ya shaidawa abokin aikin mu cewa: A hakikanin gaskiya sabon tsarin da babban bankin kasar nan ya fitar bai da wani tasiri a kan kasuwannin bayan fage kawo yanzu. Hakan kuwa bai rasa nasaba da yadda mutane basu gama fahimtar ainifin tsarin ba da kuma saukin yin canjin da kasuwar bayan fagen ke badawa.

In dai mai karatu zai iya tunawa babban bankin Najeriya watau CBN ya fito da wani tsari a kwanakin baya na cinikayyar kudaden wajen da nufi cike gibin da ke akwai tsakanin kasuwannin bayan fage da kuma halattatun kasuwannin canjin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel