Ibrahimovic ya karya wani tarihi a Manchester United

Ibrahimovic ya karya wani tarihi a Manchester United

Zuwan fitaccen dan kwallon kafar nan Zlatan Ibrahimovic kungiyar Manchester United har ya kafa tarihi a kafar yada hotunan zumunta na Instagram.

Ibrahimovic ya karya wani tarihi a Manchester United
Zlatan Ibrahimovic signs for Man Utd

Kulob din na Man Utd ya bayyana cewa wani hoton da suka saka na Ibrahimovic dauke da rigar sa ta kungiyar a shafin su na Instagram ya zuwa yanzu shine hoto daya tilo da aka fi 'so' a duk cikin jerin hotunan da kulob din ya taba sawa tun kafuwar sa.

Wata sanarwar da kungiyar ta fitar tace: "Hoton mu da muka dora a shafin mu na Instagram shine wanda aka fi so tunda aka bude shafin. Yanzu haka dai hoton yana da masoya sama da rabin miliyan tun bayan da muka sa shi a ranar 1 ga watan Juli.

"Haka ma wasu hotunan sa guda 4 da muka sa yanzu haka suna cikin wadan da aka fi so cikin 6 a duk cikin wadan da muka taba sawa a shafin namu na Instagram" Kafa wannan tarihin dai ba shine na farko ba da dan kwallon yayi tun bayan zuwan sa Man Utd din. Mai karatu zai iya tuna cewa ya karya wani tarihin ma na karfi a lokacin da ake yi masa gwajin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel