Buhari yayi magana ga sojin Kasa a Jihar Zamfara

Buhari yayi magana ga sojin Kasa a Jihar Zamfara

SHUGABA BUHARI YAYI MAGANA GA SOJIN KASA A ZAMFARA

– Shugaba Buhari na Najeriya yayi magana ga Sojin Kasa a Jihar Zamfara a ranar Laraba.

– Wannan dai na cikin Bikin ranar Sojin Kasar da aka saba yi kowace Shekara.

– Shugaba Buhari ya gabatar da wani jawabi inda ya nuna tausayin sa ga iyalan da ta’addacin makiyaya ya shafa a fadin Jihar.

– Ya kuma kara dai jinjinawa Sojin Kasa da suke aiki ba dare-ba rana

Buhari yayi magana ga sojin Kasa a Jihar Zamfara

 

 

 

 

 

 

Wani jawabi da Femi Adesina, mai ba Shugaban Kasa shawara game da harkokin yada labarai ya fitar ya (Shugaban Kasar) na cewa:

“Ina mai matukar farin cikin tsaya cikin ku a wannan raa ta yau a garin Gusau na Jihar Zamfara, ba domin komai ba, sai don rufe bikin murnar ranar Sojin Kasa na wannan Shekara ta 2016. Ina kuma mai farin cikin da aka zabi Gusau a matsayin Jihar da za a rufe wannan biki da kuma bude wani filin horas da sojin Kasa domin kawo karshen da ke wannan yaki, barnar da wadannan ‘yan ta’adda da makiyaya suka yi kan wadanda ba su ji ba-ba su gani ba, ba karama ba ce.” Shugaba Buhari ya kara da cewa: “Gagarumar nasarar da Sojin Kasa Najeriya suka samu ya nuna cewa suna da karfin tunkarar duk wata matsalar tsaro a Kasar nan.” Yake cewa: “Ina jajintawa mutanen wannan yankin da abin ya shafa, wannan abu ya sa kasuwanci da aikin noma da kuma kiwon dabbobi ya zama abu mai wahala cikin wannan kunci na tattalin arziki da muke ciki. Amma ban a shakkar cewa matakan da aka dauka za su kawo sauyi a wannan al’amari. Saboda haka ina jinjinawa Shugaban Hafsun Sojin Kasa na Kasar da wannan hangen nesa, ba shi kadai ba, har da sauran jami’an tsaro na Kasar wajen ganin yiwuwar wannan shiri. Ina kira da ku kara kaimi wajen magance duk wata matsalar tashin-tashina a wannan Kasa ta mu. Za mu cigaba da baku goyon bayan da ake bukata. Ina taya wadannan sojoji muranar kyautar da aka ba su, da kuma Sojin Kasar gaba daya wanda Shekarar sa 153 yanzu”

KU KARANTA: BUHARI A KHAKI, KO KA JI ME YAN NAJERIYA KE TA FADA!!

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel