Manchester City shirye ta ke da ta saye Dan wasa Stones

Manchester City shirye ta ke da ta saye Dan wasa Stones

LABARIN WASANNI

Kungiyar Manchester City shirye ta ke da ta saye Dan wasa Stones.

– Pep Guardiola na neman dan wasan bayan na Kuniyar Everton.

– Rahotanni sun bayyana cewa Manchester City na shirin sayen dan wasan akan fam miliayn £53.

– Idan har hakan ya tabbata, Stones zai zama dan bayan da ya fi kowa tsada a duniya.

Kungiyar Manchester City ta Ingila na shirin kafa tarihi a duniya, wajen sayen wani dan wasa. TALK SPORTS ta rahoto cewa Kulob din Manchester City za ta biya fam miliyan 53 na dalar ‘Pounds Sterling’ idan dai har ta na son ta saye dan wasan baya na Everton mai suna John Stones. Wannan zai sa Kungiyar ta Man City da kuma John Stones su kafa wani tarihi a duniyar kwallo.

Manchester City shirye ta ke da ta saye Dan wasa Stones

 

 

 

 

KU KARANTA: HENRY ZAI BAR KUNGIYAR ARSENAL

GOAL ta fuskanci cewa Kulob din na Manchester City na kokarin sayen dan wasa J. Stones daga Kulob din Everton a kakar sayayyan bana, sai dai har yanzu ba su tattauna da Kungiyar Everton din ba gar-da-gar. Majiyar mu ta nuna mana cewa, Kungiyar Everton din ta ci buri kan dan wasan nata John Stones, dalilin haka ne ake tunanin sai kulob din Manchester City ta lale makudan kudi har fam miliyan 53 na ‘Pounds Sterling’ idan har ta na son sayen dan wasan. Idan dai hakan ta tabatta, wannan zai sa John Stones din ya zama dan wasan bayan da ya fi kowa tsada a duniyar kwallon kafa, za ya wuce David Luiz na Kingiyar PSG da aka saya fam miliyan £50 daga Chelsea, shekaru kadan da suka wuce.

A SAUKE MANHAJAR MU NA Legit.ng DOMIN SAMUN LABARAN WASANNI.

Asali: Legit.ng

Online view pixel