Za’a karrama Muhammad Ali a Najeriya

Za’a karrama Muhammad Ali a Najeriya

Za’a karrama shararren dan wasan damben nan marigayi Muhammad Ali a a wani gasan dambe da gidan talabijin na Gotv zai shirya wanda zaa gudana a dakin wasa na cikin filin wasa na kasa dake Legas a ranar 30 ga watan yulio. Wadanda suka shirya gasan ne suka bayyan haka a ranar litinin 12 ga watan yulio a taron manema labarai a wurin cn abinci dake cikin filin wasa na kasa a Lagos.

Za’a karrama Muhammad Ali a Najeriya
Muhammad a yayin atisaye cikin ruwa
Za’a karrama Muhammad Ali a Najeriya
masu hada gasan

Jenkins Alumona shugaban ‘Flykite’ wanda yake mai ruwa da tsaki ne a harkan wasan damben ya fadi ma yan jaridu cewa “ba za’a taba mantawa da wanda shine mafi daukaka ba aharkan wasan dambe ba” ya kara da cewa gasan cin damben wanda shine na takwas da Gotv ta shirya zai kayatar matuka fiye da na baya. Ya ce “tabbas zamu karrama Muhammad Ali a ranar 30 ga watan yulio a gasan damben Gotv na 8.

Gasan zai kasance wuri da yan Najeriya zasu nishadantu da dambe mafi kyawun gani. “ muna da wasannin damben na shahararrun yan dambe a duk damben da za’a yi. Akwai zakaran damben rukunin tsakiya na kasa ‘Sunny King Hammer’ a gasan shekaran nan inda zaiyi kokarin kare kambunsa wanda kuma zai gwabza da zakaran damben rukunin tsakiya na yammacin Afirka ‘Rasheed Afonja Warrior Abolaji’. “zamu kuma mu kawo wasu sanannun yan wasan damben sa’annan da kananan yan dambe masu tasowa” inji Alumona.

Za’a karrama Muhammad Ali a Najeriya
Muhammad Ali a yayi

Baya da fadan neman kambun, za’a fafata tsakani zakaran dambe na rukuni karshe na kasa Olaide Fijaborn Fijabi da Joseph Blacky Joe Adeniji. Kazalika Stanley Edo Boy Eribo zai gwabza da Dele Lagelu Adele, inda kuma Waidi Skoro Usman zai buga da David Lucky Boy Ekpeyong. A wani fadan neman cin kambun damben rukunin tsakiya za’a gwabza tsakanin Mathew Wizeman Obinna da Samuel Lion Heart Igbokwe. Fada na shida a daren zai faru ne tsakanin Rilwan Babyface Babatunde da Shakiru No Shaking Lateef.

Za’a karrama Muhammad Ali a Najeriya

Zakaran gasan zai tafi gida da kyautan naira miliyan 1 da kuma kofin da aka sa don tunawa da Mojisola Ogunsanya. Har ya zuwa yanzu duniyar wasanni na cigaba da karrama Muhammad Ali tun bayan rasuwarsa a ranar Juma’a 3 ga watan yuni a asibitin garin Phoenix inda ya kwashe wasu kwanaki ana duba lafiyarsa a can.

Asali: Legit.ng

Online view pixel