Wani mutum zai kwashe watanni 18 a gidan yari

Wani mutum zai kwashe watanni 18 a gidan yari

An yanke ma wani mutum dan shekara 40 mai suna Blessing Obazuwa hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni 18 ta dalilin satan 500 KVA stableza wanda ya kai darajar kudi N35,000 da yayi

Wani mutum zai kwashe watanni 18 a gidan yari
wani mutin a ankwa

Obazuwa wanda ba da dadewa ba ya fito daga cin gidan yari inda ya kwashe shekaru 2 dalilin irin wannan laifin da ya aikata, ya amsa cewa tabbas yayi satan. Ma’aikaciyar jami’an yan sanda ,Sifeto Violet Soyemi tace abun tuhuman ya aikata laifin ne a ranar 28 ga watan yunin wannan shekaran a gidan wani Mr David Osaghae dake 21, Nova Road, Ugbowo, Benin, babban birnin Jihar Edo.

Soyemi ya fada ma kotu cewa Obazuwa na rike da makami a hannunsa shirye da aikata ta’asa. Jam’ar yan sanda tace abun tuhuman ya bayyana gaskiya yayinda aka kama shi, ta kara da cewan laifin ya sabawa sections 390(9) and 417(G) of the Criminal Code.

KU KARANTA : Buhari ya shirya ganin bayan barayin shanu

Alkali mai shari’ar kotun gargajiya ta jihar Benin, Mrs Esther Aimofumhe,tace wannan ya nuna karara cewa obazuwa bashi da niyyan canja rayuwarsa. Domin haka,ta yanke masa hukuncin cin gidan yari na watanni 6 ko ya biya N50,000 a laifin farko, da kuma zaman kurkukun shekara 1 k ya biya N50,000 a laifi na biyu.

Banda barayi irin wannan masu satan stabileza,akwai masu amfani da babur mai kafa 3 domin aikata ta’asa

Asali: Legit.ng

Online view pixel