PDP na zargin shiga da ficen da Magnus Abe

PDP na zargin shiga da ficen da Magnus Abe

–Shugabannin jam’iyyar PDP shiyar Jihar Ribas sun kawo babban kara akan senata Magnus Abe

–Jam’iyyar tace tana zargin yawan ziyarar da yake kaiwa ofishin hukumar gudanar da zabe na kasa mai zaman kanta watau INEC,da ke Abuja.

–Sanata Abe dai bai amsa zargon ba har yanzu.

Shugabannin jam’iyyar PDP shiyar jihar ribas tana zargin sanata dan jam’iyyar APC, Senata Magnus Abe, da shiga da fice da Ma’aikatan INEC.

PDP na zargin shiga da ficen da Magnus Abe
Magnus-Abe

Abe,wanda tsohon sanata da ke wakiltar mazabar Jihar Ribas ta gaba kuma dan takaran APC na zaben da za’a sake, za kasance wani kaya mai tsokale ido a Jihar tun zaben 2015 ta kasa.

A cewar wata jawabin da mai Magana da yawun shugaban PDP ta Jihar ,Bro Felix Oduah, ana zargin yawan shige da ficen da yake yi a ofishin INEC.“Abin da ban mamaki cewa, mr. abe ya kasa kama kanshi ya bar ma’aikatanhukumar INEC suyi aikin su da wuri. Wata sashen jawabin yace.

KU KARANTA : Wike ya gurfana a gaban kotu kan albashi

Haka zalika Jawabin ta bayyana cewa ita abinda ya dameta shine a’aikatan hukumar INEC suyi abinda ya kamace su domin tabbatar zabe cikin zaman lafiya da lumana. Yace :“Duk da cewan muna farge da duk wani motsin da wani an ta’aliki zai yi, ba zamu taba yarda ayi wani abin ya saba dokan rashin shin magudi ba,wajen samun sakamakon sake zabn da za’a gudanar a jihar gaba daya.

Zargin jam’iyyar PDP ta zo ne kusan mako daya bayan Sanata Magnus Abe ya fadi cewan shi fa bai amince da mai kula da harkan zaben Jihar Ribas ba, Aniedi Ikiowak. Magnus Abe ya bayyana hakan ne yayinda yake hira da manema labarai a Fatakwal,babbar birnin Jihar Ribas. Ya kara da cewa Aniedi Ikiowak dan kwangila ne a ma’aikatar ilimi a lokacin da gwamna Nyesom Wike ke mukaddashin ministan ilimi karkashin gwamnatin tsohin shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel