Yanzu! Tsagerun Neja Delta sun ce zasu fasa kwai kowa ya sani

Yanzu! Tsagerun Neja Delta sun ce zasu fasa kwai kowa ya sani

Tsagerun nan masu tada kayar baya dake a yankin Neja Delta sun fitar da wata sabuwar sanarwa inda suka tsoratar da gwamnati da cewa za su fasa kwai kowa ma yasan hakikanin gaskiyar abun da ke faruwa a yankin nasu.

Yanzu! Tsagerun Neja Delta sun ce zasu fasa kwai kowa ya sani
Tsagerun Nija Delta

Mai magana da yawon tsagerun Brig. Gen Mudoch Agbinibo ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ya raba ma manema labarai ciki hadda Legit.ng. Sanarwar tasa ta cigaba da cewa: "Yakamata kamfanin Exxon Mobile su bar yaudarar kansu suna karya. Gaskiyar magana shine jiya mun fasa masu bututun mai.

Gaskiyar zancen kenan kuma nan ba da dadewa ba ma zamu fito mu fada ma duniya dukkan abun da ake ciki. "bututun mai lamba Qua Ibe 48 shine muka fasa a jiya talata."

Tun farko dai mai magana da yawun kamfanin na Exxon Mobile ya fito ya karyata zancen na tsagerun inda yace: "Babu wani bututun mu da aka fasa, kawai karyar banza ce". Su dai hare-haren na masu tada kayar bayan tana yin matukar tasiri a kan tattalin arzikin kasar a baya-bayan nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel