Aikin Hajjin bana : Saudiyya ta hana shiga da Goro

Aikin Hajjin bana : Saudiyya ta hana shiga da Goro

–Gwamnatin kasar Saudiyya ta fitar da jawabi na hana sayar da wasu kayan abinci a aikin Hajin bana.

–NAHCON ya sanarwa Mahajjata cewa kada wanda ya shigo da goro kasar Saudiyya

–Hukumar ta sanar da cewa kada wanda ya saba wannan doka,wanda aka kama ,za’a ci shi tara.

Aikin Hajjin bana : Saudiyya ta hana shiga da Goro

Masu niyyan zuwa aikin hajjin bana yan Najeriya zasu haura da cin goro, hakan ya faru ne saboda sanarwan da hukumar aikin haji ta kasa watau ‘National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON)’ ta bayar a ranar talata. NAHCON ta sanar da hakan ne bayan ta amsa umurni daga gwamnatin kasar Saudiyya na cewa ta hana shigo da goro cikin kasar a Hajjin bana.

Hukumar tayi gargadin cewa gwamnatin Saudiyya tace zata ladabtar da duk wanda ya shigo goro, a bisa dokokin kasar. NAHCON tace : “Saboda haka,ana baiwa  duk dan najeriyan da ke nufin zuwa hajjin bana shawaran cewa abi umurnin da gwamnatin kasar saudiyya ta bada akan abubuwan da ta hana.

Hukumar ta kara da cewa hukumomin shire-shiryen aikin Hajji na Jihohi su tabbatar da cewa su fadakar da mutane akan hakan. Hukumar tace zata ci taran duk hukumar da ta saba umurnin.

KU KARANTA : Masu Zuwa Hajji Suyi Ma Kansu Tanaji – Buhari

A bangare guda, an fara shirye-shiryen rajistan masu nufin hajjin bana. An dauki hoton Mahajjata 15,531 a yanzu. An bada sanarwan cewa duk wanda ke da niyyar tafiya hajjin bana ya sallamar da fasfot din shi hukumar aikin hajjin jihohin su.

Kwanaki aka hana gwamnan Jihar Kogi, Abubakar Yahaya Bello,zuwa aikata aikin umra a kasa maitsarki saboda bizan shi tayi esfiya. Haka ya hakuri ya kwana a gidan gwamnatin Jihar Kano.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel