Thierry Henry zai bar Kungiyar Arsenal

Thierry Henry zai bar Kungiyar Arsenal

Thierry Henry zai bar Arsenal.

– Kocin Arsenal, Arsene Wenger bai amince da tayin Thierry Henry na horar da kananan ‘yan wasa ba.

– Andries Jonker ne yayi ma Henry tayin aikin horar da yaran Arsenal din.

– Thierry Henry ya tabbatar da cewa zai bar Arsenal

Thierry Henry zai bar Kungiyar Arsenal

 

 

 

 

 

 

Tsohon Gwarzon Arsenal, Thierry Henry ya tabbatar da cewa zai bar Kungiyar, ya kuma yi bayanin dalilin sa. Gawurtaccen dan wasan nan na zamanin sa, Thierry Henry yace zai bar Kungiyar ne dalilin manaja Arsene Wenger. A baya dai an rahoto cewa Henry din zai bar Arsenal ne bayan da Wenger ya ki amincewa da tayin na tsohon dan wasa Henry da ya horar da ‘yan wasan a kyauta. Yanzu dai Henry ya shiga cikin jeringiyar tsoffafin yan wasan kungiyar ta Arsenal da za su fara aikin horaswa a wani wuri.

A SAUKE MANHAJAR MU NA Legit.ng DOMIN SAMUN LABARAN WASANNI.

Jaridar Telegraph ta rahoto cewa an mika aikin horar da yan wasan kasa da shekaru-18 ga Thierry Henry. Andries Jonker, mai kula da yaran Arsenal din ne yayi ma Henry tayin wannan aiki, sai kuma daga baya Arsene Wenger yace fau-fau, hakan ba zai yi yiwu ba. Thierry Henry yake cewa: “Ina mai mika godiya ta ga Andries Jonker da yayi mani wannan tayi na horar da yan wasan kasa da shekaru-18 na Arsenal, na kuma amince da haka.” Henry ya kara da cewa: “Sai dai kuma, na fahimci matakin da Wenger ya dauka, Ina mai roka ma kocin nasu Kwame Ampadu da ‘yan wasan sa sa’a da nasara a gasar wasannin da za a shiga kwanan nan.”

Ana dai ta yada cewa tsohon kyaftin din Arsenal din, Tony Adams ne zai canji Thierry Henry.

KU KARANTA: BARCELONA TA SAYE SABON DAN WASA

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel