Buhari ya fito da sabon hanyar kawo karshen yakin Biafra

Buhari ya fito da sabon hanyar kawo karshen yakin Biafra

-Barazanar da kungiyar pro-Biafra ke yi ga harkan tsaro a kasar ya sa gwamnatin tarayya ta kafa wata kwamiti

-Kwamitin ya hada sojoji da sukayi ritaya, yan sanda da kuma wasu jami’an tsaro domin sabonta tsarin maganta matsalar tsaro daga kungiyoyin

-Hujjoji sun bayyana cewa an yanke hukunci daukan sojoji da sukayi ritaya, yan sanda da suran jami’an tsaro a kungiyar ne saboda dunbin sani da suke da shi kan harkan tsaro

Buhari ya fito da sabon hanyar kawo karshen yakin Biafra

Yawan rikici kan neman jumhuriyya Biafra ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari kafa wata kwamiti na shugaban kasa domin lura da al’amuran kungiyar pro-Biafra a kasar, mussaman yan kungiyar Movement for the Actualization of Sovereign State of Biafra (MASSOB), da kuma kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB).

Bisa ga jaridar The Sun, shugaban kasa Muhammadu Buhari a kwanan baya ya kira wani zama wanda ya samu hallartan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo,manyan ma’aikatan gwamnati da kuma sauran masu fada aji kan barazanar da tsaro ke fuskanta daga kungiyar pro-Biafra.

Bayan zaman na sirri, an yanke shawarar kafa kwamiti wanda ya hada sojoji da sukayi ritaya, yan sanda da kuma sauran jami’an tsaro domin sabonda tsarin tsari kan matsalolin tsaro daga kungiyar.

A cewar manyan sojoji da kuma majiyar shugaban kasa, an tsayar da wani janar din soja mai ritaya daga kudu maso gabas domin ya shugabanci kwamitin.

Duk da haka, ba’a sani ba ko kwamitin zasu yi kokari gurin sakin shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu kuma wanda ya asassa gidan radiyon Biafra, wanda ke fuskantar hunkuci kan zargin cin amanar kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel