IPOB sun aika da ruhohi (fatalwa) domin fansar kisan Biafra

IPOB sun aika da ruhohi (fatalwa) domin fansar kisan Biafra

-Kungiyar IPOB sunce an aika ruhin wadanda aka kashe a kasar inyamurai domin suyi farautar wadanda suka kashe su

-Kungiyar sunce an aika fatalwan mayakan aka kashe a wasu zanga-zangan lumana harda inyamurai da Fulani makiyaya suka kashe domin daukar fansar kisan su

-Sunyi gargadi cewa za’a samu wadanda suka kashe masu zanga-zangar Biafra har sai sun biya bashin laifukansu da kuma kisan kiyashi da sukayi masu

IPOB sun aika da ruhohi (fatalwa) domin fansar kisan Biafra
wadanda kisan ya cika da su

Kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) sun bayyana cewa sunyi tsafi domin fansar mayakan da hukumar tsaro suka kashe a lokacin bikin tuna ranar mutuwar gwarzayen Biafra, a ranar 30 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Igbo ta bayyana yanda Buhari ya mayar da Kanu

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, kungiyar a wata sanarwa daga mataimakin shugaban kungiyar, Uche Mefor, sunyi gargadin cewa an aika ruhin wadanda kisan kasar iyamurai ya cika da su, domin suyi farautan wadanda suka kashe su.

Shugaban kungiyar ya ce an kuma aika ruhin sauran mayakan pro-Biafra wadanda akaa kashe a sauran zanga-zangan lumana, tare da inyamurai da Fulani makiyaya suka kashe domin daukar fansar kisan.

Mefor ya ce ruhin mayakan zai ci gaba da bibiyan wadanda suka kashe su daga tsara zuwa tsara, ko wanne ta sigar da yake son daukar fansan sa har sai wadanda suka kashe su sun biya bashin laifinsu da kisan kiyashi da sukayi masu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel