Fayose ya koma ga Allah, ya shiga azumi da addau'a

Fayose ya koma ga Allah, ya shiga azumi da addau'a

–Gwamna Ayodele Fayose na Jihar Ekiti ya koma ga Allah, yayinda yayi shellar fara azumi da addu'a kwana 3,kuma yana kira ga mutanen garin su bi sahun shi.

–Yace zai yi azumi da addu'an ne saboda neman kariya nan gaba daga hadarin mota musamman daliban makaranta.

Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose,ya fara azumi da addu'an kwana 3 sanadiyar kumunan hadarin motan da ya auku a ranar litinin,11 ga watan yuli, wanda daliban jami'an ado ekiti suka rasa rayukan su. A yanzu haka, dalibai 7 ne suka rasa rayukansu sanadiyar mumunan hadarin motan.

Fayose ya koma ga Allah, ya shiga azumi da addau'a
Ayodele Fayose,gwamnan jihar Ekiti

Gwamnan ya kara da  kira ga mutanen jihar su bi sahun sa wajen addu'a uhangiji ya jikan matattu ,kuna ya cigaba da kare mu .

Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa,daliban da suka samu hadarin daliban ilimin Injiniya ne yan shekaran karshe a jami'an, sun fita ne da motar su ganin gari sai suka samu hadarin.

A wata ziyara ta nuna juyayin da gwamnan ya kai asibitin koyo ta jami'ar Jihar Ekiti, Fayose yace ya nufi yin azumi da addu'ar domin neman kariyan irin wannan hadari a nan gaba. Biyu daga cikin wadanda suka ji rauni na bakin rai ,bakin fama a asibitin.

KU KARANTA : Zamu biya albashi wannan makon – Gwamnatin Jihar Ekiti

Baya ga haka, gwamnatin Jihar Ekiti ta bayyana cewa zata fara biyan albashin ma'aikatan Jihar daga bashin biliyan N1.3 da gwamnatin tarayya ta basu,a wannan makon.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel