Yusuf da Zahra Buhari sun kammala karatunsu a Birtaniya

Yusuf da Zahra Buhari sun kammala karatunsu a Birtaniya

Yayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari Zahra da Yusuf sun kammala karatunsu na digiri cikin sa’a daga Jami’ar Surrey dake kasar Ingila. Ita dai Jami’ar ta kware wajen koyar da ilimin kimiyya, fasaha, likitanci da kuma na kasuwanci.

Yusuf da Zahra Buhari sun kammala karatunsu a Birtaniya
Iyalan Buhari

Haka kuma Jami’ar ta kasance cibiyar binciken tauraron dan adam da na sadarwa. Sa’annan Jami’ar wakiliya ce a cikin kungiyoyin daban daban da suka hada da kungiyar Jami’o’in kasashen rainon Ingila, kungiyar Jami’o’in nahiyar turai da dai sauransu.

Yusuf da Zahra Buhari sun kammala karatunsu a Birtaniya
Zahra Buhari rike da takardar shaidar kammala karatun ta

Ana ma Jami’an kallon tana daya daga cikin manyan jami’o’in kasar Ingila, kuma darajan na hauhawa a jerin jadawalin jami’o’in kasar.

Darussan da darajansu tafi na sauran sune: darasin yawon bude ido, shari’a, fsahar lantarki, kimiyyan abinci, darasin karantar al’umma, fasahar sararin samaniya, fasahar kerere, fasahar gine gine, fasahar kemical, darasin tsimi da tanadi da kuma darasin sanin halayen dan adam.

Yusuf da Zahra Buhari sun kammala karatunsu a Birtaniya
Yusuf Buhari rike da takardar shaidar kammala karatun shi

Jim kadan da yaduwan labarin, jama’a da dama sun bayyan ra’ayinsu game da lamarin a shafukan yana gizo, ga kadan daga cikin su.

“yanzu dai yusuf sai ya ara ma mahaifinshi shaidar kammal karatunsa, tun da an gama kashe masa kudin kasa”

Wani kuma yace “dama yarinyar nan tana zuwa makaranta? Na dauka tana fashi” wani yace “na tabbat ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu sun fara aika musu takardun aiki, alhali wasu sun kammal karatu tun 1998 har yanzu basu da ikin yi”.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel