Da kyar kakata ta sha daga masu kisa – Harry Song

Da kyar kakata ta sha daga masu kisa – Harry Song

Shahararren mawakin nan Harrison Tare Okiri, wanda aka sani da suna Harrysong, ya bayyana dalilin sa na yin gangamin wasan wakoki da yake Kira Harrysong Peace Concert a Asaba.

Da kyar kakata ta sha daga masu kisa – Harry Song

Cikin jawabin da mai magana da yawunsa Desmond Ike Chima, yayi, yana mai cewa kakarsa na da hannu cikin dalilinsa na yin wasannin.

Shi dai mawakin salon Reggae Blues, yana mai cewa "kakata, wadda na fi kaunarta fiye da duk duniyar nan ta sha da kyar daga hannun matasa masu kisan ature a unguwarmu.

"Rikici ya barke game da rigimar filaye inda aka rika kone gidaje tare da mutanen da ke cikinsu. Abin ya tayar mani da hankali yayin da kakata ke bani labarin yadda ta sha ta kyar".

Asali: Legit.ng

Online view pixel