Yan sanda sun kama Uba da tona kabarin yaronsa

Yan sanda sun kama Uba da tona kabarin yaronsa

–An kama wani mutum dan shekara 25 da kan dansa.

–Uban yaron ya hada kai da wani abokinsa ne wurin aikata ta’asan

Jami’an yan sanda  sun kama wani dan ta’aliki dan shekara 25,mai suna Maikudi Mohammed a garin misau,karamar hukumar Misau ta Jihar Bauchi, da kan mutum. Bisa ga maganan da kakakin jami’an yan sanda,Haruna Muhammad , yayi, yace mutumin tare da abokinsa sun haka kabarin yaron bayan an birne shi a kauyen Galambi domin sayar da shi.

Yan sanda sun kama Uba da tona kabarin yaronsa
Maikudi Mohammed da Damina Mohammed

Yaron da aka tone kabarin sa,haifaffan cikin Mr Mohammed ne wanda ya rasu kwanakin da suka gabata. Yan sanda sun cfke shi yayinda suka sami labarin hakan.

Kakakin jami’an yan sanda yace : “ A Bisa binciken da muka gudanar da farko, mun gano cewa mai laifin ya hada baki da wani abokinshi,mai suna damina mohammed,mai shekara 26 ,kuma yan karamar hukumar misau,a Jihar Bauchi. Sun je makabartar garin Galambi ,suka tone kabarin yaron,suka ciro gawar,suka cire kansa domin sayar ma wani .

Mai laifin ya tona asirin kanshi cewa kabarin yaronsa,haihuwar cikin sa ne da ya rasu ba da dadewa ba, amma ya koma makabarta ya tone kabarin sa.

KU KARANTA : Wike ya jagoranci yaki da masu satar mutane

Har yanzu dai ana cigaba da gudanar da bincike akan al’amarin kuma za’a gurfanar da duk wanda aka kama da hannu a ciki.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel