Fulani makiyaya sun kai hari jihar Niger, sun kashe mutane 11

Fulani makiyaya sun kai hari jihar Niger, sun kashe mutane 11

-Fulani makiyaya sun kai hari jihar Niger

-An rahoto cewa makiyayan sun kasha mutane 11 a sabon harinsu

-Sun kai sabon harin ne lokacin bikin sallar Eid El-Fitri

Fulani makiyaya sun kai hari jihar Niger, sun kashe mutane 11

A zubar da jinni tsakanin Fulani makiyaya da al’umman Gbagyi a jihar Niger wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 11. An bayyana cewa al’amarin ya faru ne a lokacin bikin sallar Eid El-Fitr. An ruwaito cewa mutane 4 ne suka rasa rayukan su a Lamba karamar hukumar Paikoro, yayin da yayin da aka kuma kashe mutane 7 lokacin wani rikici tsakanin yankabilar a Barakuta, karamar hukumar Bosso na jihar.

KU KARANTA KUMA: An dawo da naira billiyan N1.5 da aka binne a gonaki a Abuja

Jaridar Punch sun ruwaito cewa a Barakuta, bayan rasa rayuka da aka yi, mutane da dama sun samu raunuka, anyi asarar dukiyoyin, miliyoyin naira, harda gidaje, asa wa  ababen hawa, da motoci wuta. Ba’a tabbatar wa masu labarai mussababin abunda ya haddasa rikicin ba. Duk da haka, gwamnan jihar Abubakar Sani Bello, ya sha alwashin yin nazari da kuma gano musabbabin abunda ya hadassa rikicin.

Yayi Magana a lokacin da ya ziyarci makarantar firamari na Bosso, Bosso inda aka ajiye mata da yara daga Bara-Kuta na dan wani lokaci. Abun jimami an yi asarar rayuka da dukiyoyi, hada da gonaki, gwamnan yace: “babu wanda ke da ikon daukan ran wani.

A halin yanzu, shugaban karamar hukumar  Paikoro, Mr John Maikarfi ya fada wa gwamnan cewa ya shirya wani kwamiti na mazaje 9 domin suyi bincike kan abunda ya haddasa rikicin a kauyen Lamba. Kwamandan yan sanda na jihar, DSP Bala Elkana, ya kuma bayyana wa manema labarai cewa an zuba yan sanda tare da sojoji a garuruwan domin su hada gwiwa gurin kewaye garin, kari da cewa ana binciken wadanda aka kama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel