Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai hari Neja, sun kashe mutum 11

Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai hari Neja, sun kashe mutum 11

Anyi wani mummunan fada tsakanin wadanda ake zargin makiyaya ne da gwarawa a jihar Neja wadda yayi sanadiyar mutuwan mutane 11.

Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai hari Neja, sun kashe mutum 11

An samu labarin cewa lamarin ya afku ne yayin bukukuwan sallan Idi. An ruwaito an kashe mutum 4 a Lamba na karamar hukumar Paikoro, inda kuma aka kashe wasu mutum 7 a wata hatsaniya data taso tsakanin wasu yan kabila daya a Barakuta cikin karamar hukumar Bosso. Jaridar Punch ta ruwaito cewa ban da kasakashe da akayi a Barakuta, an raynata mutane da dama, anyi asarar dukiya ta miliyoyin nairori ciki hard a gidaje, sa’annan an kone motoci da Babura da yawa.

Zuwa yanzu dai ba’a san dalilin da ya kawo rigiman ba, sai dai Gwamna Abubkar Bello ya sha alwashin kamo masu laifin. Yayi wannan jawabi ne a lokacin da ya kai ziyara makantar firamare na Bosso inda aka tsugunar da yara da mata wadanda hatsaniyar ya koro su daga Barakuta

Cikin nuna kaduwa ganin irirn asaran rayuka da dukiyoyi da akayi, Gwamnan yace “babu wani dake da ikon kashe wani, ba zamu yarda ko mu kyale irin wannan kisan gillan ba. Babu yadda za’ayi ka dauki adda ka kashe wani mutum kawai don kun samu sabani, akwai doka kuma ba wanda ya isa yafi karfin doka”

Ya kara da cewa “koma dai wani irin abani mutum ya samu da wani, bai kamata ya dauki doka a hannun sa ba. Na baiwa shuwagabannin kananan hukumomin da abin ya shafa, kwamishinan yan sanda da kuma mataimakina na musamman  akan harkan tsaro izinin gudanar da bincike kan al’amarin don gano wadanda suka aikata ta’asan tare da hukunta su. Da gaske muke mu kawo karshen irin wannan aika-aika, hukumar yansanda tare da sauran hukumomin tsaro su tabbata an gano bakin zaren wannan matsalar, kuma a kamo masu lafin a hukuntasu.”

Gwamnan ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar data tabbatar an baiwa yan gudun hijiran cikakken kulawa, sa’anan ya umarci yansanda da su basu kariya a matsugunin nasu.

“nayi matukar tausaya muku dangane da wannan ibtila’i daya faru a garin Lamba, tunda an samu zamn kafiya yanzu, ina rokon ku da kowa ya koma bakin aikinsa ba tare da wano fargaba ba. Gwamnatin na kokarin maganin matsalar, kuma zamu tabbaatar da tsaron rayuka da dukiyoyin mutanen mu” Gwamnna ya bai ya al’ummar Lamba wannan tabbacin.

Sai dai shugaban karamar hukuman Paikoro John Maikarfi ya fada ma gwamna cewa ya kaddamara da wata kwamitin mutm 9 da zata binciki hatsaniyar. Ita ma hukumar yansanda jihar Neja ta hannun mai magana da yawunta mataimakin sifeto Bala Elkana ya fada ma yan jaridu cewa an tura yansand da sojoji zuwa kauyukan da abin ya faru don yin sintiri, ya kara da cewa wandanda an fara binciken wadanda aka kama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel