Hausawa ba sa kyamar ‘yan Igbo – Sarki Sunusi

Hausawa ba sa kyamar ‘yan Igbo – Sarki Sunusi

 -Sarakin Kano ya ce hausawa da ‘yan kabilar Igbo na zaune lafiya

-Hausawa sun dade suna mu’amillar kirki da ‘yan Igbo

- rashin fahimtar da ke tasakanin kabilun biyu aikin magabta ne

Hausawa ba sa kyamar ‘yan Igbo – Sarki Sunusi
Mai marataba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II ya ce al’ummar hausawa ba sa kyamar ‘yan Igbo mazauna jihar Kano.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, Sarkin ya fadi hakan ne a ranar Litinin 11 ga watan Yuli a lokacin da ke karbar shugaban majalisar sarakunan jihar Abia, Cif Ebere Chidik a fadarsa, Mai martaba sarkin ya kuma kara da cewa, “mu hausawa sama da shekaru masu yawa mun kasance muna zaune da ‘yan kabilar Igbo ba tare da kiyayya ko hassada ko kuma keta ba...don haka da akwai bukatar da kabilun biyu su fahimci irin baiwar da Allah Ya yi wa kowannensu….”

Sarkin ya kuma kara da cewa duk wani rashin fahimta da gutsiri tsoma da tsegunguma tsakanin kabilun biyu aikin ‘yan gaza-gani ne, wanda a cewarsa, su ke kokarin ganin an samu sabani a tsakanin su a birnin na kasuwanci mai tsohon tarihi.

A jawabinsa tun da farko, Cif Ebere ya ce sun zo fadar ne domin yin gaisuwa ga sarkin, da kuma mika godiyarsa ga sarakin bisa irin rawar da ya ke takawa wajen  daidaita tsakanin kabilar Igbo mazauna jihar da kuma hausawa.

A kwanan baya ne aka kasha wata ‘yar kabilar Igbo a kasuwa a bisa zargin yin batanci ga Manzo mai tsira da amincin Allah. Wanda hakan ya kusa tayar da fitina a jihar.     

 

 

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel