Karanta yadda Ronaldo ya bayyana Jin dadinsa

Karanta yadda Ronaldo ya bayyana Jin dadinsa

 - Ronaldo ya bayyana rashin Jin dadinsa na fita wasan.                 

 -Portugal sunci faransa inda hakan ya basu Daman daukan kofin EURO na shekar 2016.       

 -Kaftin din na Portugal ya bayyana murnansa nacin gasar.

Dan wansan Real Madrid Kuma dan kasar Portugal ya bayyana tabbacin da yake da ita akan Yan wasan portugal din a wannan gasar na EURO 2016.

Ronaldo dai ya fita daga wasan ne tun kafin aje hutun Rabin lokaci, Amman dukda haka ankai minti chasa'in babu wanda yaci wani, inda wasan yakai ga buga extra time inda dan wasa Mai suna Eder daya shigo bada dadewa ba ya samu daman cin kwallon Mai mahimmanci cikin minti 109 inda suka samu damar lashe gasar, masu masaukin bakin dai Sunyi kokarin ramawa amman mai tsaron gidan portugal din mai suna Patricio ya hanasu inda wasan ya kare portugal din taci faransa daci daya da nema.

Karanta yadda Ronaldo ya bayyana Jin dadinsa
Ronaldo

 

Ronaldo ya bayyana cewar Yayi murna Sosai Sosai, domin kuwa wannan abune daya dade yana jira a rayuwarsa tun shekar 2004.

A cewar sa “na roki Allah Ya sake bani dama, na Kara dacewa, duk da abubuwa basuyi min kyauba yadda nakeso, najima kaina ciwo da kaina tun a farkon wasa, amman na yarda da abokan wasana domin kuwa suna da duk abunda ya kamata Yan wasa su samu sannan Kuma da yadda kocin mu yake gudanar da tsarin wasan sa.

KU KARANTA : Renato Sanches, Griezmann sun lashe manyan kyautuka

Haka kuma Ronaldon ya damu kwarai da gaske domin kuwa a kullun burinsa yaga kasar sa ta dauki Kofi tare da shi domin ya kafa tarihi a rayuwarsa. Yanzu na samu daman hakan a cewarsa, na gode ma Allah, Abubuwa Sunyi mana kyau. Dan wasan ya karkare bayaninsa dacewar sunci kasar faransa yaji dadi Sosai, wannan shine lokacin dayafi kowane lokacin Jin dadi a rayuwarsa ta kwallon kafa. Yan kasar portugal din sun cancanci hakan haka kuma Yan wasan kasar suma sun cancanci hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel