An sallami manyan Jami’an gidan yari guda 2

An sallami manyan Jami’an gidan yari guda 2

Hukumar kula da gidan yari ta kasa ta sanar da sallamar mayan Jami’an ta su biyu daga aiki.

Ta bayyan hakanne a wata takarda da ta fito daga mai Magana da yawun hukumar Francis Enobore inda ta ce an sallami manyan jami’an ne bayan wata ganawar gaggawa da aka yi tsakanin jami’an tsaron farin kaya, da jami’an kwanakwana, jami’an shige da fice da kuma jami’an ganduroba. Enobore ya ce ganawar kuma ta biyo bayan nadin da aka yiwa Ja’afaru Ahmed ne a matsayin shugaban hukumar kula da gidajen yari na kasa.

An sallami manyan Jami’an gidan yari guda 2
Jafar Ahmed Shugaban hukumar kula da gidajen yari na kasa

“takardar da ta samu sa hannun sakataren hukumar Alhaji A.A Ibrahim a ranar 28 ga watan Yuni 2016 tayi nuni da cewa an yanke shawarar sallamar ma’aikatan ne domin sun grime ma sabon shugaban hukumar a matsayi, kuma haka ne ka’idan hukumar soja da kuma hukomimin masu kayan sarki”

Manyan jami’an sun hada da Aminu Sule mataimakin kwanturolan, da mataimakin kwantrulan bursuna na biyu Ali Bala. “muna musu fatan alheri, kuma hukumar ta yaba da irin gudunmowar da suka bayar wajen cigaban ta” a cewarsa. A ranar asabar 25 ga watan Yuni ne dai aka samu wasu mutane da suka tsere daga gidan yari na Kuje dake babban birnin Abuja.

A yayin da kafafen watsa labarai suka cika da labarin cewa Charles Okah wanda yake tsare a gidan yarin akan lafin tada bam da akyi a ranar murnan samun yancin Najeriya ne ya tsere daga gidan yarin.sai dai a cikin wata sanarwa da hukumar ta bayar tace daurarrun su biyu sun tsere ne daga dakunan su a yayin wata karamar hatsaniyar da yammacin ranar Juma’a 26 ga watan Yuni. A wani lamari na hukunta wadanda abin ya shafa don hana afkuwar hakan a gaba hukumar kula da gidajen yarin kasar nan ta dakatar da jami’anta su 14. Enobpre ya ce dakatarwar ya faru ne bayan sakamakon wani binciken daya gudana akan tserewar ta ranar 25 ga watan yuni.

Wadanda hukuncin ya shafa sun hada da : DCP Musa Tanko, SIP Buhari Dogo, PIP Stephen Edogbanya, PIP Patrick Teru; IP Usman Peter; IP Dennis Makum, IP Fassan Akin; SPA Daka James; SPA Adamu Luka; SPA Zakari Yunasa; PA Asnamal Samuel; PA Ejegwa Patrick; PA 11 Isah Ibrahim, and PA 11 Ngede Salifu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel