Badakalar Takalman Buhari - Abuja ta maganta

Badakalar Takalman Buhari - Abuja ta maganta

-Fadar shugaban kasa ta mayar da martani akan surutan da yaduwa a kafafan labarai cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya takalman da kudin su ya wuce N200,000.

-Wannan jita jitan ya tayar da zaune tsaye na cewan mutane, shugaba Buhari gaskiya yake fadawa yan Najeriya ba akan arzikin sa.

Badakalar Takalman Buhari - Abuja ta maganta
Bashir Ahmad tare da shugaba Muhammadu Buhari

Yayinda wasu kuma suka ce ,a matsayin shi na Shugaban kasa, shi ya cancanta ya sanya takalma mafi kyawu komin tsadan su, ama kuma ,wasu sun cigaba da cewa shugaba Buhari na amfani da kudin harajin mutane yana kashe su, yayinda tattalin arzikin kasa ta fadi.

Amma daya daga cikin ma'aikatan fadar shugaban kasa, Bashir Ahmad,ya fito yayi magana akan jita jitan ,tace Shugaban kasan ya saye takalmin kafin zaben 2015.  Ahmad,da ya bada martanin ta shafin sadarwarsa ta twita,ya bayyana cewa irin wadannan labarai,kamata yayi ayi banza dasu,amma yayi maganan ne saboda wadanda suka fara labarin su rubuta cewan kafin zabe ya saya. Amma ma'aikatacin fadar shugaban kasan ya goge maganar sa a shafin ,amma an dauki hoton maganan kafin ya goge.

KU KARANTA : Adesina ya bayyana wasu abubuwa masu ban mamaki

Baya ga haka, mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin Neja Delta, Birgediya Janar Paul Borih (Mai ritata), ya bayyana damuwarsa akan jinkirin gwamnatin tarayya wajen biyan tsaffin yan bindigan neja delta.

A wata jawabin da ya aka baiwa Hukumar Samar da labarai ta Najeriya, wacce Piriye Kiyaramo ya sanya hannu, Boroh wanda ya ke mai gudanar da shirin ya bayyana bacin ransa akan jinkirin hiyan kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel