Wani dan Real Madrid yayi ritaya saboda ciwon zuciya

Wani dan Real Madrid yayi ritaya saboda ciwon zuciya

Wani matashin dan wasan Real Madrid Lucas Silva ya yi ritaya da buga kwallo saboda ciwon zuciya dake damun sa

Wani dan Real Madrid yayi ritaya saboda ciwon zuciya
Lucas Silva

Dan wasan dai yana daf da zuwa kulob din Sporting Lisbon ne a matsayin dan aro inda aka gano yana da cutar don haka komawar tasa bata yiwuba. Dan wasan dai shine ya bayyana ritayar tasa ta shafin zumuntar sa na Instagram inda ya rubuta: "Na yi iya bakin kokari na, yanzu kuma na gama. Na dauki dangana."

Tun farko dai kungiyar tasa ta asali watau RealMadrid ta amince tare da takwarar ta ta Sporting Lisbon wajen yin aron dan wasan amma daga bisani sai abun ya faskara bayan da aka gano ciwon zuciyar. Silva dai ya zo kulob din Realmadrid ne a shekarar 2014 akan kudi £10m kuma an sa ran zai kawo karshen matsalar dan wasan dake bugama Realmadrid din tsakiya.

Daga baya ne kuma aka kai shi aro shekarar data gabata a kulob din Marseille.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel