Dogara ya koka da rashin shugabanci nagari

Dogara ya koka da rashin shugabanci nagari

-Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya samu lambar yabo ta Zik ta wannan shekarar

-Kakakin ya ce shugabanci ne babbar matsalar kasar nan

-Ya ba da shawarar gina makarantun da za su rika koyar da yadda ake shugabanci

 

Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya dora alhakkin rashin ci gaban kasar na a kan rashin shugabanci nagari.

 

Dogara ya koka da rashin shugabanci nagari
Hon. Yakubu Dogara

Kakakin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke karbar lambar yabo ta shugabancin al’umma ta tunawa da marigayi Dakta Nnamdi Azikiwe a wani kasaitaccen biki da aka yi jihar Lagos a daren Lahadi.

Dogara ya ce shugabancin na gari ne zai tsamo kasar nan daga matsalolin da suka addabe ta, kuma muddin aka samu nasarar samar da hakan, hakika za’a samu waraka kuma Najeriya za ta zama son kowa. Kakakin ya kuma kara da cewa gwamutsa kasar nan da Turawan mulkin mallaka suka yi ba kuskure ba ne, sai dai baiwa ce daga Allah, baiwar da muka kasa amfani da ita domin ci gaba.

Kakakin majalisar ya yi kira da a kakkafa makarantun da za koyar da matasa da muhimmancin shugaban ci nagari, ganin cewa tsarin makarantun yanzu Turawan mulkin mallaka ne suka kafa su domin samar da ma’aikata. Sannan ya yi kira ga shugabani na yanzu, da su gina ‘yan baya da za su gaje su wajen samar ayyuka na gari.

A lokacin da kakakin majalisar ya karbi jakadar kasar Sudan Ibrahim Busha a ofishinsa a Abuja ranar 1 ga watan Maris, ya koka da rashin ci gaban da shugabancin na nagari ya janyo wa kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel