Tsagerun Neja Delta sun dau alwashin sai sun hana Buhari fita

Tsagerun Neja Delta sun dau alwashin sai sun hana Buhari fita

– Kungiyar ta ce watsi da Shugaban kasan yayi da maganan sulhu ne ta jawo hakan.

–  Sun sha alwashin cigaba da durkukusar da tattalin arzikin kasa.

– Sun karyata maganan cewa Tompolo ke daukan nauyin su.

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa Tsagerun Neja Delta za su hana shugaban kasa fitar da ma fetur daga yankin . Yan bindigan basu gushe na suna kai hare-hare kafufuwan man fetur da ke yankin Neja delta. Sun sha alwashin cewa tunda shugaban kasa,Muhammadu Buhari yayi banza dasu,baza su daina fusata gwamnatin shi ba. Bugu da kari ma, sun ce zasu fi da tayar da hankali tunda Shugaban kasa yafi son yaki akan sulhu.

Tsagerun Neja Delta sun dau alwashin sai sun hana Buhari fita
tsagerun neja deta

Yan bindigan sun karyata zancen cewa tsohon shugaban yan bindiga ,Government Tompolo , wanda aka fi sani da Tompolo ke daukan nauyin su.

Wata kungiyar yan bindigan mai suna Niger Delta Revolutionary Crusaders (NDRC),ta bayyana cewan ita ta shiga yaki da gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin kasar Saudiyya domin sa hannunta cikin al'amuran Najeriya. Hakazalika kungiyarIjaw People Development Initiative (IPD),ta jaddada cewa ya zama wajibi gwamnati ta saurari maganan mutanen.

Wannan rahoton na zuwa ne jim kadan bayan kungiyar Niger Delta Red Squad, ta ce sai ta koya ma yan najeriya darasi ta hanyar nakasa kafufuwan mai.

KU KARANTA : Yankin Neja Delta ta fi ribatar gwamnatin Buhari- Minista

Kungiyar yan bindigan da ta taso daga garin Ohaji Egbema ta Jihar Imo,tayi gargadi da gwamnatin jihar imo cewa idan fa wa'adin tsagaita wutar su na makonni 2 ya kare, zasu tayar da hankalin jihar. Kungiyar ta bayyana hakan ne ta shafin sadarwarta ta Facebook. Kungiyar ta kara da cewa tana ayyukan su saboda nuna kiyyayan ta akan zalunci da ake yiwa mutanen yanki masu arzikin man fetur.

 

 

 

 

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel