An kama yan Boko Haram a wani coci a jihar Lagas

An kama yan Boko Haram a wani coci a jihar Lagas

-An kama yan ta’dadan Boko Haram a jihar Lagas

-An mayar da su jihar Borno inda suka fito

-An kama daya daga cikin su ya boye a coci

An kama yan Boko Haram a wani coci a jihar Lagas

Masu tsaro a jihar Lagas sun kama wasu yan ta’addan Boko Haram tare da dayan su da ya boye a wani coci. Jaridar Vanguard ta rahoto cewa yan kungiyar ta’addan shidda yan farar hular Civilian Joint Force suka kama a sashi daban daban na birnin.

An ruwaito cewa bayan  harin da sojoji suka kai a jihar Borno domin yakar yan kungiyar yan ta’addan, sun tashi daga karamar hukumar Bama, Baga da kuma Konduga na jihar.

KU KARANTA KUMA: Dasuki ya zargi Jonathan kan dala biliyan 15 na makamai

Wadanda ake zargin sun ba da sunan su a matsayin Ibrahim Ali, Abubakar Ahmed, Babagana Blam, Goigoi Kamsalem, Ibrahim Mohammed da kuma Adams.

Alhaji Mustapha Mohammed wanda shine shugaban kungiyar task force, Mai-Kanuribe na jihar Lagas, da kuma sarkin Hausawan masarautar Ijora, sun bayyana cewa an kama Ibrahim Ali,da Babagana Blam wadanda suke yan karamar hukumar Bama, da Konduga a Isheri-Ojodu Berger, yayinda aka kama Goigoi Kamsalem, Ibrahim Mohammed yan karamar hukumar Bama, da Abubakar Ahmed na karamar hukumar Baga, a inda suka boye a Victoria Island.

An kama na shiddansu ne a inda ya boye a wani coci dake garin Festac.

Mohammed ya bayyana cewa kungiyar sa ta yadu a karamar hukumomi 57 a jihar Lagas da jihar Ogun, kuma suna kai hari tun shekaru biyar. Yace suna aiki ne da yan kungiyar Boko Haram. Ya ce an kama su ne bisa ga hikima, kuma cewa an kama yan kungiyarsa  da dama a baya, an kuma mika su a hannun yan sandan jiha wato Department of State Service, yan sandan sun mayar da su Maiduguri, Jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel