Abu 5 da Portugal zatayi don ta doke Faransa

Abu 5 da Portugal zatayi don ta doke Faransa

Yau lahadi dai ne kasar Portugal zata buga wasan karshe na biyu na gasar cin kofin kasashen turai tun kafuwar ta ita da mai masaukin baki kasar Faransa. Wannan wasan dai shine kadai tsakanin gwarzon dan kwallon nan na kasar Portugal Cristiano Ronaldo da kuma mafarkin sa na jagorantar kasar sa zuwa ga cin kofi.

An dai fi kyautata zaton kasar ta Farasa ce zata lashe kofin bayan da suka lallasa kasar Germany a wasan su da ya gabata. Faransar tana da shahararrun yan wasan da suke taka muhimmiyar rawa sosai a gasar da suka hada da Antoine Griezmanm, Dimitri Payet da ma Oivier Giroud wadanda dukkanin su suka zura kwallaye da dama zuwa yanzu.

Yanzu dai ga wasu dabarun da ake sa ran kasar Portugal zatayi anfani da su don su doke kasar ta Faransa.

1. Sanya Pepe: indai har kasar ta Portugal tana so ta kare bayanta sosai to kam sai ta sanya shahararren dan wasan kulob din RealMadrid din don kuwa haduwar sa da Jose Fonte na kulob din Southampton tana yin kyau.

 

2. Kada a ba Giroud sarari: duk da cewa dan kulob din na Arsenal bai zura kwallaye da yawa ba amma ya taimaka sosai wajen nasarorin da kasar ta samu musamman ma wajen taimaka ma Griezmann. Indai Portugal na son kare mutuncin ta to dole ne ta hana dan wasan sarari.

 

3. Hana Payet shiga gidan gol: wannan kam zai dan yi wahala amma dole ne sai an yi hakan indai Portugal na son ta lashe gasar. Dole ne a sa yan wasan tsakiya da yawa don a hana shi Payet din motsi mai karfi ma.

 

4. A rike Griezmann a koda yaushe: wannan dan wasan ya nuna basirar sa sosai a wannan gasar don kuwa yaci kwallaye. Dan kwallon yana da dubarar zamewa daga jikin yan baya don haka da kwace kwallo sai ka ganshi shi kadai. Wannan ne ma babban dalilin da yasa Faransar ta cire Germany.

 

5. Bi ta wurin Evra: Inda kawai ke da dan taushi-taushi a duk bayan Faransa shine ta inda Evra ke tsarewa. Dan wasan na kulob din Juventus dai ya sha ansar dorowan kati cikin gasar. Dole ne kasar ta Portugal tayi dubarar jawo masa katin yadda zai dan samu rauni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel