Dangote ya maganta kan tattalin arziki

Dangote ya maganta kan tattalin arziki

Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote y aba da tabbacin cewa za’a samu haske a karshen rami, sakamakon kokarin da gwamnatin tarayya ke yi don kawo ci gaba sauran bangarorin tattalin arzikin da ta bari a baya saboda man petir.

Babban dan kasuwan wanda yayi Magana tare da mambobin kungiyar masana’antar sa da suka kai masa ziyara a lokacin bikin sallar Eid el-Fitr ya bayyana cewa, halin da kasar take ciki a yanzu yazo ne sakamakon dogaro da tayi kan man petir kan sauran bankarori, kuma faduwar farashin man petir a kasuwar duniya shima ya taimaka gurin faruwan haka.

Dangote ya maganta kan tattalin arziki

Ya ce duk da haka, tattalin arzikin kasar zata koma daidai sakamakon yunkurin da gwamnati mai ci a yanzu keyi, wanda zai kawo ci gaba bawai a matsayin kasa mai dogaro da kai kawai ba, amma harda hanyoyin samu wanda zai kawo ci gaba a rayuwan mutanan kasar.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya buga sunayen barayin kasa – Aborishade

Dagote ya yi kira kan cewa ci gaban ba wai zai zo a lokaci guda bane, “ zai dauki lokaci, amma akwai tabbacin cewa rayuwa mai inganci na nan zuwa. Ya zama dole mu kara hakuri kuma mu ba da gudunmuwar mu, domin gwamnati bazata iya yin haka ita kadai ba."

Dangote ya bayyana cewa arewacin kasar na da kyau gurin noma, don haka ya zama dole gwamnatin jihar su yi kokari gurin kawo ci gaba a fannin. Kasar china wacce take da mafi yawan tattalin arziki a duniya a yau bata kai kasar Najeriya kyan gurin noma ba.

Dangote ya bayyana kudirinsa na samar da ayyuka 200,000 a ma’aikatar sa a fannin noma a arewacin jihar tsakanin yanzu zuwa shekara ta 2018.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel