Manchester City ta sanar da gagarumin cinikin dan wasa

Manchester City ta sanar da gagarumin cinikin dan wasa

Tsohon dan wasan tsakiyan Borussia Dortmund zai kasance wani ginshiki da duk wani shiri kocin Manchetser City Pep Guardiola.

Iklay Gundogan ya bayyana cewa Manchester City ta kammala cinikin siyan sa na tsawon shekaru 4, a baya dai an samu rohoto da jaridar Bild da tace cewa mai horar da kungiyar Manchester City Pep Guardiola zai hadu da wakilin Ilkay Gundogan.

 

Manchester City ta sanar da gagarumin cinikin dan wasa
Ilkay Gundogan

Yace “saura kiris in tafe Manchester united a bara, said a ba komai ne kake so ba zai faru. Watakila ba lokacin daya dace in tafi ba kenan, daga karshe sai muka yanke shawarar in kara kwantaragin shekara 1.” Gundogan ya kara “mun yawan tattaunawa akan batun da Dortmund muka yarda akan in tafi, ba zan tafi ba tare do an siye nib a, don haka sai na sabonta kwantaragi na, yanzu kam a bana kowa na murna lamarin ya kawo karshe”

Ya kara da cewa “a watanni kadan da suka gabata ne na fahimci ya kamata in samu canji don in kara nuna kaina a idon duniya. Hakan yasa nayi farin cikin kasancewa ta anan domin samu daman hulda da Guardiola da wannan kungiya”

Asali: Legit.ng

Online view pixel