Shugaban Hukumar JAMB na cikin tsaka mai wuya

Shugaban Hukumar JAMB na cikin tsaka mai wuya

Kwamitin gudanarwa na Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandari na Najeriya tare da shugabanta Farfesa Dibu Ojerinde na cikin tsaka mai wuya yayin da kungiyar Malaman Jami’o’in kasarnan ta sa wando daya da su akan sabon tsarin hukumar na daukan dalibai a manyan makarantun kasarnan.

 

Shugaban Hukumar JAMB na cikin tsaka mai wuya
dalibai a yayin zana jarabawar JAMB

Kungiyar ASUU na ganin hukumar ta wuce gona da iri wurin fitar da sabon tsarin, a maimakon ta kyale Jami’o’I sun tantance yadda ya kamata su gudanar da al’amuran makaranta. Shugaban ASUU reshen Jami’ar Ibadan, Deji Omole yace an taba amfani da sabon tsarin a Jami’ar Ibadan na tsawon shekaru 5, amma daga baya aka watsar dashi.

Kungiyar ASUU tayi bore ga sabon tsarin, inda tace tsarin zai dakile yayan talakawa ne daga shiga makarantun gaba da sakandari ne. a wata sanarwa da ASUU ta fitar tace da alama Shugaban Hukumar da kuma Ministan Ilimi Adamu Adamu sun shiga cikin rudani.

Omole ya koka yana cewa Misnistan da Shugaban sun kasa zama kaifi daya, domin a baya basu goyi bayan karban kudi da sunan kudin jarabawar share fagen shiga Jami’a, sai kuma yanzu suka kawo wani maganan biyan kudin tantancewa a cikin sabon tsarin da suka fidda.jaridar Daily times ta ruwaito Omole yana cewa anyi sabon tsarin ne kawai don ya amfani yayan attajirai ba yayan talakawa ba, ya kara da cewa Ministan tare da Shugaban Hukumar suna yi kamar basu san halin da ake cikin ba a Jami’o’in kasarnan.

A cewar Omole, kungiyar ASUU zata nuna tirjiya ga dukkan wani shiri da zai dauke wa Jami’o’i cin gashin kan su da kuma ikon majalisar koli ta Jami’o’I na su gudanar da tsarin daukan dalibai. Ya ce “hukumar JAMB tana fita daga huruminta, na ta shirya jarrabawa kuma ta saki sakamon haka. Majalisar koli ta Jami’a itace keda ikon samar da tsarin daukan yaran da JAMB ta turo mata. Kowane Jami’a nada ma’auninta, wanda bas a karkashin ikon wani wakilin Gwamnati”

Ya kara da cewa “JAMB bat a daman fada ma Jami’o’i yadda ya kamata su dauki dalibai, wannan wani hanya ne baoye gazawarsu, don an dade an shakkar sahihanci ita kanta hukumar JAMB din. Shuwagabannin hukumar JAMB da ita kanta JAMB din na cikin rudu ne kawai.”

Abin da yafi bani mamaki shine game da cin jarabawar da hukumar JAMB ta shirya, “a bara sun tura sunayen yara zuwa Jami’o’I masu zaman kansu, don su faranta ma abokansu, yaran nan kuwa yayan talakawa ne da basu zabi makantun nan ba.” Ya ka da cewa “kazalika ma a bana, cikin jarabawar da aka yi a bayannan, sun kara ma yara maki 40  ba tare da wasu dalilai ba, a dalilin haka wadanda suka yi jarabawa biyu da kuma wadande ke jiran sakamon jarabawar kammala sakandari zasu cutu. “za’a samu karuwar almundahana hukumar shirya jarabawar kammala sakandari ta WAEC don mutane zasu yi kokarin siyan sakamako mafi kyau, tunda hakan ne kawia zai tabbatar da samun gurbi a makanrantun gaba da sakandari. “wuarren jarabawa inda ake satar amsa zasu yawaita a dalilin tsarin nan, wanda ke nuna cewa Minista da shugaban JAMB sun ci nasara wurin tabbatar da cin hanci da rashawa, kuma hakan zai kara durkusar da karatun jami’a a Najeriya

Ya karkare zancen sa da cewa “kungiyar ASUU na goyon bayan cin gashin kai na Jami’o’i. hukumar JAMB ba tad a ikon samar da tsarin duakan dalibai, sai dai ma a sake yi JAMB din garanbawul domin a inganta da mutunta sakamon jarabawarsu. Tun bayan sanar da daina jarabawar sharen fagen shiga Jami’a ‘Post-UME’Jami’o’i da dama sun samar da sabbin tantance dalibai masu neman shiga jami’o’i don su cigaba da samun kudaden shiga, alhali kuma dalilin da yasa kenan aka hana gudanar da tsohon jarabawar ”

Asali: Legit.ng

Online view pixel