Badakalar cinikayya: Ni banda laifi inji -inji Neymar

Badakalar cinikayya: Ni banda laifi inji -inji Neymar

Dan wasan geben kungiyar Barcelona dake kasar Spain Neymar ya kara jaddada cewar shi fa bai da laifi a bisa zargin da ake yi masa na kumbiya-kumbiya a cikin cinikayyar sa da kulob din nasa.

Badakalar cinikayya: Ni banda laifi inji -inji Neymar
Marc Bartra, Neymar, Lionel Messi and Sergi Roberto

Shi dai dan kasar Brazil din ana tuhumar sa ne tare da mahaifin sa a kan yadda suka yi rufa-rufa wajen cinikin dan wasan da takai tsabar kudi har €57m daga Santos zuwa Barcelona. Neymar din dai ya bayyana a farfajiyar kotun da ake tuhumar tasa tare da mahaifinsa inda ake ci gaba da sauraron shari'ar tasa. Ana yin shari'ar ne a garin Madrid -babban birnin kasaar ta Spain.

Da yake zantawa da manema labarai, Neymar din yace: "Ni banda laifi haka ma mahaifina. Ina ganin ana tuhumar mune sakamakon rashin cikakkun bayanai akan al'amarin baki daya. Kokuma kawai wasu ne da basu son mu suke kara hura wutar".

"Ni na yarda dari-bisa-dari da mahaifi na kuma shine ya shiga gaba wajen cinikayyar." Yanzu ma ina jin dadin ganin sa kusa dani". Shi dai dan kwallon na Barcelona Neymar yanzu haka yana shirin kara tsawon kwantaragin sa da kulob din nasa kuma shine zai jagoranci tawagar yan kwallon Brazil din zuwa gasar Olympics da za'a fara cikin watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel