Tuwita ta rufe shafin nan na tsagerun Neja Delta

Tuwita ta rufe shafin nan na tsagerun Neja Delta

Kamfanin sadarwar zumunta na tuwita ya rufe shafin nan na tsagerun Neja Delta ban da akayi ta kai su kara wajen shugabannin kamfanin.

Tuwita ta rufe shafin nan na tsagerun Neja Delta
Tsagerun Nija Delta

An dai rufe shafin ne a yau litinin 4 ga wata. Yanzu haka dai idan aka shiga shafin yana nuna: "An rufe wannan shafin. Duba nan don gani tare da sanin dalilin da yasa aka rufe shafin ko kuma ka/ki koma shafin ka/ki"

Su dai tsagerun sun sha anfani da shafin nasau na tuwita wajen sanar da daukar alhakin hare-haren da suka kai a kan bututun mai da dama dake yankin nasu. Tsagerun abaya kuma suna anfani da shafin nasu wajen isar da sakonni ko tsoratar wa zuwa ga gwamnatin tarayya dama kamfunnan mai dake yankin nasu.

A wani labari kuma Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya gargadi gwamnatin tarayya da jami'an ta akan yadda suka yakar tsagerun a yankin nasu. An ruwaito Gwamnan dai ya gargadi musamman shugaban rundunar sojojin ruwan kasar lokacin da ya karbi bakun cin sa a gidan gwamnatin jihar inda ya gargadeshi da suyi taka-tsan-tsan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel