Naira ta sauko N342/$1 daga N345/$ a Kasuwan canji

Naira ta sauko N342/$1 daga N345/$ a Kasuwan canji

Gidan Jaridar Legit.ng na bada rahoto tabbacin cewa kudin Najeriya ta dan kara daraja da N3 a bisa dalar Amurka a kasuwan canji. Kudin Najeriyan ta hau ne a ranar Juma'a , 1 ga watan Juli zuwa N345/$ , ta sauko N342/$ a kasuwan canji a yau 4 ga watan Yuli.

Samun karfi ya faru ne a sakamakon rahoton da aka samu ceea babban bankin tarayya CBN zata lashe amanta , zata cigaba da sayar ma yan kasuwan canji dalar Amurka. An samu cewan cigaba da rage darajar da naira keyi sanadiyar rashin dalan ne a kasuwan canji.

Naira ta sauko N342/$1 daga N345/$ a Kasuwan canji

Wata majiya a kasuwan canji ta bayyana ma Legit.ng cewa : “An samu dala da yawa a yau a cikin kasuwan canji saboda an samu rahoton babban bankin tarayya CBN za ta fara sayar mana da dala. Saboda haka, masu dala a hannu na sayar da shi , domin sa ran zasu samu a hannun CBN”.

KU KARANTA : EFCC ta gano N2.5Miliyan a asusun ‘yar aikin gidan Minista

 

Legit.ng na tuna muku cewan babban bankin tarayya CBN ta dakatar da sayar ma yan kasuwan canji dala, a watan janairu, saboda fadin tattalin canjin kasan. Babban bankin tarayya CBN kuma a watan da ya gabata, ta kirkiro wata sabuwar manufan canji. Wannan manufa ta halalta ma mutane sayan dalar Amurka a bankuna.

Ku kasance da Legit.ng wajen sani juye juyen canji a koda yaushe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel