Jarumi ya fuskanci Boko Haram shi kadai (Hotuna)

Jarumi ya fuskanci Boko Haram shi kadai (Hotuna)

-Jarumin jami’in da ya rasa aikin sa da kuma hanyan cin abincin sa don fada da mayakan Boko Haram matashi ne

-yaje da sunan sa Muazu Alhaji Misiya

-Misiyi dan Arewa ne

Jarumi ya fuskanci Boko Haram shi kadai (Hotuna)

A lokacin da mayakan Boko Haram suke ganiyan su, Misiyi ya rasa aikinsa kuma saura kadan ya rasa rayuwansa ga mayakan, kawai don gannin cewa an samu zaman lafiya Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Yana da matan aure guda biyu da yaya shidda.

Misiyi na zaune a karamar hukumar Bama a jihar Borno. Yayi aiki a First Bank dake a garin Maiduguri. Duk da haka, ya rasa aikinsa a bankin sakamakon yana so ya yaki yan ta’addan Boko Haram. Bayan nan, ya shiga kungiyar Civilian Joint Task Force don ganin ya taimakawa sojojin Najeriya a kokarisu na ganin sun share mayakan Boko Haram daga yankin arewacin kasar Najeriya.

KU MARANTA KUMA: Tashin hankali: Fulani makiyaya sun far ma jihar Plateau

A satin da ya wuce, mun samu cewa sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar yan farar hulan JTF sun ceto kusan mutane 5,000 daga hannun Boko Haram. Tunda Misiyi ya shiga kungiyar yan farar hular JTF, bai hut aba. Yace ba zai kasa a gwiwa ba har sai yaga dukkan mayakan sunje kasa a yankin arewa. Ya kara da cewa idan har fadan ta ci gaba har muddin rai, shi ma zai ci gaba.

A yayin da yake ci gaba, baban yara shidda yace mayakan Boko Haram sunyi duk yanda zasuyi don ganin sun kashe shi amma basuyi nasara ba. Mutanan Bama da Maiduguri sun bashi matsayin ‘gwarzon yaki’ saboda gudunmuwar da ya bayar gurin yaki da yan ta’addan da kuma taimako gurin rage barazanar yan kungiyar Boko Haram.

Bincike ya nuna cewa Misiyi bai karbi ko kwabo ba a matsayin albashi ba daga hannun sojoji ko gwamnatin tarayyan Najeriya ko jihar Borno tunda ya shiga kungiyar. Ga hotunan Misiyi a kasa:

Jarumi ya fuskanci Boko Haram shi kadai (Hotuna)
Mu'azu Alhaji Misiya
Jarumi ya fuskanci Boko Haram shi kadai (Hotuna)
Jarumi ya fuskanci Boko Haram shi kadai (Hotuna)
Mu'azu Alhaji Misiya
Jarumi ya fuskanci Boko Haram shi kadai (Hotuna)
Misiya

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel