Hukumar NPS: An dauki ‘Yan Arewa da dama a boye

Hukumar NPS: An dauki ‘Yan Arewa da dama a boye

NPS: An dauki ‘Yan Arewa da dama a boye

– Bincike ya nuna cewa an saba dokar Kasa wajen daukar ma’aikatan hukumar gidan yari

– Kashi 68 bisa 100 da aka dauka, ‘Yan Arewa ne

– Ana kokarin rufe maganar

Hukumar NPS: An dauki ‘Yan Arewa da dama a boye

 

 

 

 

 

 

 

 

Bincike ya nuna cewa yawanci mutanen da aka dauka aiki a hukumar kula da gidan yarin Kasar (Watau NPS), ‘Yan Arewancin Kasar ne. Cikin sababbin ma’aikatan da aka dauka aiki guda 538 Karkashin Shugaban Hukumar gidan yarin Kasar, Ahmed Jafaru da kuma Ministan cikin gidan Najeriyar, Abdurrahman Dambazzau, ya saba dokar Kasa wajen daukan ma’aikata.

KU KARANTA: KU BAR KUKA, INJI SHUGABAN OPC.

Binciken ya bayyana cewa akwai jerin sunaye kashi 2 da aka dauka aikin, wadanda za a horar da su makamashin aiki a Garin Kaduna da Legas. Jerin na farko na dauke da sunayen wadanda za a horar da su a Gidan kolejin horar da ma’aikatan gidan yari na Kiri-kiri da ke Birnin Legas. Jerin na biyu kuma mai taken “Jerin Sunayen sababbin dauka na watan Yuni, 2016”, za a horar da wadannan sahu ne a Gidan kolejin horar da ma’aikatan gidan yari na Garin Kaduna. Mutane 370 dai da aka dauka cikin 530 sun fito ne daga Arewacin Kasar, kenan wannan ya nuna cewa kashi 68% na daukan sun fito daga bangaren Jihohi 19 na Arewacin Najiyar. Sai dai jami’in da ke magana da yawun-bakin hukumar ta NPS, Mista Francis Enobore yace ba zai iya magana dangane da daukar sababbin ma’aiakta ba a yanzu. Sai dai yace, babu yadda za a yi a horar da mutum ba tare da an dauke sa aiki ba.

KU KARANTA: YAN KUDU SUN NUNA DAMUWAR MAI DA SU SANIYAR WARE

Majiya daga hukumar gidan yarin Kasar (watau NPS) sun bayyana mana cewa ma’aikatan hukumar suna kokarin rufe maganar daukar ma’aikatan. Haka dai majiyar ta ke nuna cewa, tabbas, sababbin ma’aikata aka diba, domin kuwa babu yadda za ayi ace hukumar za ta horar da ma’aikatan ta har fiye da 500. Shi dai Mista Enobore yace dole za a bi ka’ida wajen daukar sababbin ma’aikata, domin sai an sanar da Gwamnatin Tarayya idan akwai wani gibi, haka nan kuma dole hukumar da ke kula da daukar ma’aikatan Tarayya sun tabbatar da cewa ba a fifita wata kabila ba ko Jiha. Wannan daukar ma’aikatan dai yayi kama da wanda babban bankin Kasar yayi a kwanakin baya.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel