An kai wa dan wasan Barcelona hari gidan sa 

An kai wa dan wasan Barcelona hari gidan sa 

Ana zargin wasu gugun magoya bayan Croatia da kai wa dan wasan tsakiya na Barcelona Ivan Rakitic hari a gidan sa dake wani tsibiri na Ugljan na kasar Croatia yayin da yake shakatawa.

An kai wa dan wasan Barcelona hari gidan sa 

Jaridar Vercernji List dake garin Zagreb ta ruwaito cewa wasu matasa ne su shida suka yi ta jifa da dutse a gidan nasa har suka fasa masa taga da kofa kafin daga bisani su ruga. Wannan dai ya tilastawa iyalan na Rakitic barin gidan minuta 30 bayan faruwar lamarin ta jirgin ruwa.

Bayan faruwar hakan ne kuma daga baya sai dan wasan mai shekaru 28 ya rubuta a shafin sa na zumunta na Instagram cewar abun da ya faru ba zai hana shi nishadi ba shi da iyalan sa. Ya rubuta: "Gani ina shakatawa da iyalina. Babu wanda zai bata mana hutun mu ya hana mu dariya" tare da dora hoton sa shi da matar sa da diyar sa..

Mai karatu zai iya tuna cewa dan kwallon yana cikin tawagar da ta wakilci kasar tasa a cikin gasar cin kofin kasashen turai da ake yi yanzu haka inda su kasar Portugal ta koro su. Ana tsammanin Rakitic din zai koma kulob din sa na Barcelona karshen watan nan na July don ci gaba da buga kwallon sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel