Kungiyar kwallon kafa ta Watford ta kammala cinikin dan wasa

Kungiyar kwallon kafa ta Watford ta kammala cinikin dan wasa

Kungiyar kwallon kafa ta Watford ta kammala cinikin dan wasan gaban kulob din Granada na kasar Spain watau Isaac Success akan kudi £12.5m. Shi dai wannan dan wasan dan Najeriya ne.

Kungiyar kwallon kafa ta Watford ta kammala cinikin dan wasa

Rahotanni dai sun nuna cewa an kammala cinikin dan wasan ne tun farkon shekarar nan amma sai a ka jinkirta bayyana wa har zuwa yanzu. Kulob din na Granada ya sha fama kakar wasa ta bara don kar ya fada gurbin gajiyayyu. Shi dai dan wasan mai shekaru 20 an yi ta alakanta zuwansa kungiyoyi da dama ciki hadda PSG da Inter Minal amma wakilin sa Dominic Egbukwu ya dage kan cewa dan wasan ya je Watford.

Wakilin nasa dai ya shedawa jiridar nigeriasoccer.com a watan Fabrerun da ya gabata cewa: kulob din Atletico, Inter da PSG duk sun nuna sha'awar su ta dan wasan. Kai hadda ma wasu daman." "Amma su kulob din na Granada basu son su saida ma kowa shi in ba Watford ba".

Shi dai Success ya zura kwallaye 5 ne cikin wasanni 30 da ya buga kakar wasannin da ta gabata. Idan har ya koma Watford din to zai yi kokowar samun riga ne daga hannun Troy Deeney da kuma Odion Ighalo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel